Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da fara aiwatar da dokar hana amfani da motocin da ake rufe lambobinsu, da kuma wadanda ba su da lambar.
A wata sanarwa da kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya fitar, ya ce matakin ya fara aiki nan take a fadin jihar Kano.

Rundunar ta ce rufe ko cire lambobin mota na hana jami’an tsaro gano motocin da ake amfani da su wajen aikata laifuka kamar fashi da makami, garkuwa da mutane, da safarar miyagun kwayoyi.
Gwamnatin Kano ta yi wa Kwankwaso bankada kan kudin fansho
Sanarwar ta ce za a kwace motocin da suka karya dokar tare da gurfanar da direbobinsu a gaban kotu, ba tare da sassauci ba.
‘Yan sanda sun kuma bukaci masu ababen hawa su tabbatar da cewa motocinsu suna da ingantattun lambobin masu rajista a gaba da baya, tare da cire duk wani abin da ke hana ganin lambobin a fili.

Rundunar ta jaddada cewa ba a ɗauki matakin don a takura wa wasu ba, sai dai don inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Kano.