Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗin sabbin masu ba shi shawara na musamman tare da sauya wa wasu daga cikin masu rike da mukaman da ke aiki a halin yanzu wuraren aiki.
A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadaura24 a ranar Alhamis, ya ce matakin wani ɓangare ne na sake fasalin tsarin gudanarwar harkokin gwamnati domin ƙarfafa aiki da kuma inganta ayyukan gwamnati a jihar.
A yayin sauye-sauyen, gwamnan ya soke ofisoshin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Cikin Gida da kuma Mai Ba da Shawara na Musamman kan Ofishin gwamnan na Abuja, inda aka sauya musu da wasu ayyuka.

An mayar da Habiba Mustapha Barwa, wadda ke rike da mukamin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Cikin Gida a Gidan Gwamnati, zuwa Mai Ba da Shawara na Musamman kan Ayyuka na Musamman bangaren Mata .
Haka kuma, Umar Uba Akawu, wanda ya kasance Mai Ba da Shawara na Musamman kan Ofisoshin Hulɗa, an mayar da shi Mai Ba da Shawara na Musamman a Cabinet Ofis kan Harkokin Siyasa.
Sauran wadanda aka sauya wa mukamai sun hada da Akibu Isa Murtala, wanda ya koma Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Ma’aikata daga mukaminsa na baya a bangaren gudanarwa; Ibrahim Adam, wanda aka sauya daga harkokin yada labarai zuwa harkokin sada zumunta; da kuma Nasiru Isa Dikko, wanda aka mayar daga harkokin kungiyoyi masu zaman kansu zuwa bangaren tallafawa al’umma.
Gwamnan ya kuma amince da naɗin Bello Nuhu Bello a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Gudanarwa a Ofishin Gwamna. Kafin wannan naɗi, Bello ya kasance Babban Mataimaki na Musamman kan harkokin Gudanarwa.
Haka nan, an nada tsohon Sakataren Yada Labarai na jam’iyyar APC a Kano, Ahmed Muhammad Aruwa, a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai. An kuma nada Buhari Sule Kura a matsayin Mai Ba da Shawara na Musamman kan Kungiyoyi Masu Zaman Kansu (NGOs), yayin da Yahuza Ado Yankaba ya samu karin girma daga Babban Mataimaki na Musamman zuwa Mai Ba da Shawara na Musamman kan Tashoshin Mota.
Sauran sabbin wadanda aka nada sun hada da Ahmed Tijjani Musa, Ibrahim Hamisu Rimi, Mustapha Abdullahi Rabiu Kura, Injiniya Bashir Abdullahi Kutama, Naziru Abdullahi Karaye da Tahir Ado Rabiu.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce an yi wannan sauye-sauyen ne domin inganta harkokin gudanarwa tare da daidaita ayyukan hukumomin gwamnati da manufofin gwamnatinsa.
Ya taya sabbin wadanda aka nada murna, tare da kira gare su da su tabbatar da yin aiki tukuru .