Shugaban RATTAWU Kano Ya Jagoranci Yan Kungiyar Ziyarar Ta’aziyya Ga Iyalan Marigayi Adamu Ibrahim Getso

Date:

Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Rediyo, Talabijin, Wasan Kwaikwayo, Fasaha da Al’adu (RATTAWU) reshen Jihar Kano, Kwamared Babangida Mahmouda Biyamusu, tare da mambobin Majalisar Zartarwa ta ƙungiyar, sun kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Alhaji Adamu Ibrahim Getso, tsohon Darakta Janar na ARTV kuma tsohon Manajan Darakta na Radio Kano, wanda ya rasu bayan fama da rashin lafiya.

Ziyarar ta kasance ne domin jajanta wa iyalan mamacin tare da nuna alhini kan babban rashi da aka yi a harkar yaɗa labarai da al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.

IMG 20251224 WA0004

Da yake jawabi yayin ziyarar, Kwamared Babangida Mahmouda Biyamusu ya bayyana rasuwar Alhaji Adamu Ibrahim Getso a matsayin babban gibi ga masana’antar yaɗa labarai, yana mai cewa marigayin ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa al’umma, wayar da kai da kuma horar da ƙwararrun ma’aikatan yaɗa labarai tsawon shekaru.

Ya ce marigayin ya kasance mutum mai ƙwarewa, nagarta da kishin aiki, wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasa gidajen rediyo da talabijin a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

Shugaban RATTAWU ya ƙara da cewa kyawawan halaye da ayyukan alherin da marigayin ya bari za su ci gaba da zama abin koyi ga masu tasowa a harkar aikin jarida da watsa labarai.

A madadin RATTAWU reshen Jihar Kano, Kwamared Babangida Mahmouda Biyamusu ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan mamacin, abokan aikinsa, ɗalibansa da daukacin al’ummar jihar, tare da addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya yalwata masa rahama, Ya sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa, sannan Ya bai wa iyalansa da masoyansa juriyar jure wannan babban rashi.

IMG 20260504 WA0036(1)
Talla

A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na Kungiyar Mustapha Idris Yola ya sanyawa hannu kuma aka aikowa Kadaura24 sun yi addu’ar Allah Ya jiƙan Alhaji Adamu Ibrahim Getso, Ya sa Aljanna ce makomarsa. Amin.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sanata Barau Ya Nuna Kwarewa da Ƙwazo a Majalisar Dattawan Najeriya

Daga cikin abubuwan da ke bayyana nagartar ɗan majalisa...

Kano ce ke kan gaba a rajistar katin zabe a Nigeria – Kwamitin kar-ta-kwana

Gwamnatin Jihar Kano ta ce jihar na ci gaba...

Gwamnatin Kano Na Nazarin Kafa Kamfanin Jiragen Sama Mallakin Jihar

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa tana duba yiwuwar...

Fassarar jawabin Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu na ranar Dimokradiyya

SAKON SHUGABA BOLA AHMED TINUBU A RANAR DIMOKURAƊIYYA TA...