Daga Abdallahi Shu’aibu Hayewa
Kungiyar Dalibai ta Makarantar Mariri wato Mariri Student Association ta gudanar da gagarumin taron duba lafiyar al’umma kyauta tare da wayar da kan al’ummar yankin, domin karfafa musu gwiwa wajen kula da lafiyarsu don gano cututtukan dake damun mutum domin daukar matakin gaggauwa.
Da take ganawa da Jaridar Kadaura24 shugaban kungiyar Daliban ta Mariri Kwamared Aminu Danladi ya bayyana cewa manufar taron ita ce domin su tallafawa al’umma musamman masu karamin karfi da ba su da damar yin gwaje-gwajen asibiti akai-akai.

Kwamared Aminu Danladi ya ce wannan mataki wani bangare ne na ci gaba da shirye-shiryen kungiyar wajen tabbatar da cewa al’umma sun san muhimmancin kula da lafiya, da yin gwaje-gwajen duba lafiyarsu akai-akai domin kare kansu daga kamuwa da cututtuka masu tsanani.
Ya kara da cewa kungiyar za ta ci gaba da gudanar da irin wadannan shirye-shirye a lokuta daban-daban domin ciyar da al’umma gaba ta fuskar kula da lafiya da ilimi.
A nasa jawabin Dagacin Mariri Alhaji Saminu Madaki ya nuna jin dadinsa tare mika godiyarsa ga wannan kungiyar ta daliban Maririn, bisa wannan kokarin da sukayi.
Gwamnan Taraba ya bayyana dalilinsa na shirin komawa APC
” Babu shakka Wannan aikin da wannan kungiyar ta yi wa al’ummarmu abun a Yana ne, kuma Muna kira ga sauran kungiyoyi Irin wadannan da zu yi koyi da Wannan kungiya domin tallafawa al’umma masu karamin karfi”. Inji Dagacin
Wasu daga cikin wadanda su ka amfana da wannan shirin sun bayyana farin cikinsu bisa wannan aiki, tare da mika godiya ga kungiyar saboda irin gudunmawar da take bayarwa wajen tallafa wa lafiyar jama’a a yankin.
A yayin taron, an gudanar da muhimman gwaje-gwaje da suka haɗa da, Gwajin cutar Hanta, Hawan Jini da kuma Gwajin Ciwon shuga, Wanda ya samu Halartar Iyaye Maza da mata.