Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya ce zai shiga jam’iyyar APC a ranar 19 ga Nuwamba.
A wata tattaunawa da ‘yan jarida a ranar Asabar, gwamnan ya bayyana a hukumance cewa zai bar jam’iyyar PDP zuwa jam’iyya mai mulki.
Kefas ya ce sauyawar jam’iyyar “na da nasaba da makomar mutanen Taraba.

“Za a sami babban sauyi da daidaituwa a ranar 19 ga Nuwamba,” in ji gwamnan.
“Zan sauya sheka a hukumance daga PDP zuwa APC. Wannan sauyi yana da alaka kai tsaye da makomar al’ummar Taraba.”
Kefas shi ne sabon gwamna na baya-bayannan da ya bar PDP zuwa APC a shekarar 2025.
Sauran gwamnonin da suka sauya sheka daga PDP zuwa APC sun hada da Umo Eno na Akwa Ibom, Sheriff Oborevwori na Delta, Peter Mbah na Enugu, da Douye Diri na Bayelsa.
A 2023, Kefas ya lashe zaben gwamnan Taraba da kuri’u 257,926.
Ya doke Muhammad Yahaya na jam’iyyar NNPP da Emmanuel Bwacha na APC.
Tun daga 1999, duk gwamnonin Taraba sun kasance ‘yan jam’iyyar PDP.