Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, murnar zagayowar ranar haihuwarsa ta shekaru 70.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Litinin.
Shugaba Tinubu ya yaba da gagarumar gudunmawar Shekarau ga ci gaban ƙasa, yana bayyana shi a matsayin malami, jami’in gwamnati, da ɗan siyasa mai jajircewa wajen hidimar al’umma.

Shugaban Ƙasan ya tuna yadda Shekarau ya fara aikinsa a matsayin malamin makaranta kafin daga baya ya kai matsayin Babban Sakatare a Ma’aikatun Jihar Kano, sannan ya shiga siyasa a farkon shekarun 2000. Ya kuma yaba da nasarar da Shekarau ya samu a zaɓen shekarar 2003 da kuma irin mulkin jinƙai da ya gudanar a tsawon wa’adin mulkinsa na shekaru takwas.
Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026
Tinubu ya kuma jaddada rawar da tsohon gwamnan ya taka a matsayinsa na Ministan Ilimi daga shekarar 2014 zuwa 2015, da kuma a matsayin Sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya daga 2019 zuwa 2023.
Shugaban Ƙasan ya nuna godiyarsa ga Shekarau bisa jajircewarsa da hidima ga ƙasa, tare da yin addu’ar Allah Ya ba shi ƙoshin lafiya da tsawon rai domin ya ci gaba da hidima ga al’ummar Kano da Najeriya baki ɗaya.