Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Date:

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria  Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya bayyana cewa hukumar ta rage kudin aikin hajjin bana, inda ya koma naira miliyan 7.6 daga jihohin Arewacin Nijeriya.

Farfesa Abdullah Sale Pakistan ya bayyana hakanne ga manema labarai a makka.

Jihohin Adamawa da Borno za su biya Naira miliyan 7.5  ne ya shaida wa Hausa haka daga kasar Saudiyya.

InShot 20250309 102512486

Ya ce rage kudin hajjin ya koma haka ne sakamakon umurnin shugaban Nijeriya na samar da ragin kudin da kuma tattaunawar da suka yi ta baya bayan nan da kamfanonin Saudiyya.

A karkashin sabon farashin yanzu jihohin da ke shiyyar Borno/Adamawa za su biya Naira 7,579,0202 sabanin naira 8,327,125 da hukumar ta sanar a baya.

Sauran jihohin Arewa kuma sabon farashinsu shi ne naira 7,669,769 sabanin naira 8,457,685 da aka sanar a watannin baya.

Jihohin kudancin Nijeriya kuwa za su biya naira 7,991,141 sabanin naira 8,784,085.

Sai dai yanzu an kayyade ranar 05 ga watan Disamba ta zama ranar karshe da duk mai sha‘awar zuwa hajji daga Nijeriya zai biya kudinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...