Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru da Bebeji ya sanar da dawowa jam’iyyar APC tare da bayyana cikakken goyon bayansa ga kokarin sake neman wa’adin shugabancin kasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Jibrin, wanda ke wakiltar mazabar Kiru da Bebeji a Jihar Kano, ya fitar a ranar Litinin.

A ranar Lahadi ne ya sanar da ficewarsa daga NNPP da kuma darikar Kwankwasiyya wacce tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ke jagoranta.
An tarbe shi cikin girmamawa da farin ciki daga dubban magoya bayansa a garinsu na Kofa, karamar hukumar Bebeji, inda ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Shugaba Tinubu.
Fiye da malamai 2,000 sun gudanar da addu’o’i na musamman domin Shugaba Tinubu da neman zaman lafiya da ci gaba ga Jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026
Dawowar Jibrin cikin APC na zuwa ne bayan watanni biyu da korarsa daga NNPP bisa zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya da kuma kin biyan kudin harajin jam’iyya.
Ya bayyana godiya ga jam’iyyar NNPP bisa goyon bayan da ta ba shi a baya, sannan ya roki magoya bayansa da su bi sahunsa wajen shiga wannan sabuwar tafiya tare da jam’iyyar APC.