Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da ƙaddamar da sabon harajin shigo da kaya na kashi 15 cikin 100 kan dukkan man fetur da dizil din da aka shigo da shi zuwa Najeriya..
An bayyana cewa wannan mataki na gwamnati na da nufin kare matatun man fetur na cikin gida da kuma daidaita kasuwar man fetur ta ƙasa, sai dai ana hasashen zai iya haifar da ƙarin farashin mai a matakin farko.
Wannan umarni na Shugaban Ƙasa na ƙunshe ne a cikin wata wasika da aka aika ta zuwa ga hukumar tara haraji ta Ƙasa da hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa domin aiwatar da sabon tsarin nan take.

Wasikar, wacce mai taimakawa Shugaban Ƙasa, Damilotun Aderemi, ya sanyawa hannu , ta nuna cewa an amince da shirin ne bayan shawarar da shugaban hukumar haraji Zacch Adedeji, ya gabatar.
A cikin shawarar da ya mikawa shugaban ƙasa, Adedeji ya bayyana cewa harajin zai shafi kimar kaya,da inshora da kuɗin jigilar na dukkan mai da ake shigo da shi, domin daidaita farashin shigo da mai da na cikin gida.
Gwamnatin Kano Ta Karyata Rahoton Cibiyar Wale Soyinka Kan Take ‘Yancin ‘Yan Jarida
Ya ƙara da cewa wannan mataki wani ɓangare ne na ci gaban sauye- sauyen gwamnati domin ƙarfafa tace mai a cikin gida, da tabbatar da
daidaiton farashi, da kuma ƙarfafa tattalin arzikin mai bisa kuɗin naira, bisa tsarin sabunta fata na gwamnatin Tinubu don tabbatar da tsaron makamashi da dorewar tattalin arziki.