Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta bayyana cewa rahoton da ake yadawa cewa an gina wani filin jirgin sama na boye a jihar Kebbi domin safarar miyagun kwayoyi, labari ne na bogi da aka kirkira ta hanyar fasahar AI (Artificial Intelligence), wanda bai wanzu a zahiri ba.
Wannan bayani ya fito ne bayan umarnin shugaban hukumar, Janar Buba Marwa (mai ritaya), wanda ya umurci rundunar NDLEA ta jihar Kebbi da ta gudanar da bincike kan zargin cewa akwai wani filin jirgin sama a dajin Argungu da ake amfani da shi wajen safarar kokain daga Najeriya zuwa Bogota, Columbia.
Kwamandan NDLEA na jihar Kebbi, Rabi’u Abdullahi Sokoto, ne ya bayyana haka a taron manema labarai da aka gudanar tare da Kwamishinan Bayanai da Al’adu na Jihar Kebbi, Yakubu Ahmad Birnin Kebbi, a yammacin ranar Laraba.

“Bisa umarnin shugaban hukumar, Janar Marwa, mun tura jami’anmu zuwa wurin da ake zargin akwai filin jirgin sama. Amma babu wani irin abu makamancin haka a dajin da ake magana a kai,” in ji Kwamandan.
Ya kara da cewa:
“Bincikenmu ya gano cewa babu wani mutum a jihar da ake kira Ibrahim Musa, tsohon mataimakin kwamptrola na kwastam, wanda ake zargin shi ne ya gina filin jirgin.”
“Ta yaya ake cewa wani filin jirgin sama da ba a san shi ba zai iya daukar jirage 12 lokaci guda? Bidiyon da ake yadawa an kirkire shi ne ta hanyar fasahar AI don karkatar da hankali daga wasu dalilai.”
A nata bangaren, Kebbi Police Command ta bayyana labarin a matsayin mara tushe da makama, tare da kiran sa da “yunkurin bata sunan jihar Kebbi da rundunar ‘yan sanda.”
Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Wadanda Za a Yi Wa Afuwa
A cikin wata sanarwa da CSP Nafi’u Abubakar, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Birnin Kebbi, ya sanya hannu, rundunar ta bayyana cewa wannan rahoto na bogi ne da aka kitsa domin haifar da fargaba da rage kwarin gwiwar jami’ai wajen yaki da laifuka.
A nasa jawabin, Kwamishinan yada labarai ta Jihar Kebbi, Yakubu Ahmed, ya bayyana rahoton a matsayin karya, rashin hankali da abin dariya.
“Wannan wani bangare ne na zarge-zargen banza da wasu ‘yan siyasa masu son mulki ta kowace hanya ke yadawa domin bata sunan Gwamna Nasir Idris da mutanen jihar Kebbi,” in ji shi.
“Wannan aiki ne na rashin gaskiya da halin rashin kishin kasa. Ba sa damu da illar da hakan zai iya jawo wa jihar muddin burinsu na siyasa ya cika.”
Kwamishinan ya roki jama’ar jihar Kebbi da su yi watsi da irin wannan jita-jita, tare da gargadin cewa: “Makiyan jihar za su ci gaba da ƙoƙari, amma kar mu basu dama su yi nasara.”
VON