Daga Dantala Uba Nuhu, Kura
An kawo ƙarshen shari’ar wata tunkiya da ta jawo cece-kuce har ta kai ga gurfanar da mutune bakwai a gaban Kotun Shari’ar Musulunci ta Garun-Malam, ƙarƙashin jagorancin Alkalin kotu, Malam Naziru Abdullahi Tanburawa.
An shafe kimanin sati hudu ana gudanar da wannan shari’a, wacce ta samo asali daga rikicin mallakar wata tunkiya da aka saya a kasuwar Kura.
A yayin zaman kotun na ƙarshe, mai gabatar da ƙara, Insifekta Nasiru Abubakar Dan-Sakkwato, ya sake gabatar da waɗanda ake zargi, da suka haɗa da ɓangaren masu sayen tunkiyar tun daga farko, tare da wani Bafulatani mai suna Alhaji Mai-Saje wanda ke ikirarin cewa shi ne mamallakin dabbar da ake magana a kanta.

Kotun ta cika makil da ‘yan kallo yayin zaman, ciki har da Shugaban Ƙungiyar Fataken Dabbobi na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Ahmed Ɗan-Shana, wanda ya bayyana cewa yana bibiyar shari’ar tun daga farko saboda batun ya shafi ɗaya daga cikin ‘ya’yan ƙungiyarsu.
Haka kuma, daga ɓangaren Fulani, Alhaji Jimau Hardo, wanda shi ma ke ɗaya daga cikin jagororin Fulani a Karamar Hukumar Kura, ya halarci zaman domin ganin yadda za a kammala shari’ar da ta daɗe tana jawo cece-kuce.
A yayin sauraron ƙarar, Alkalin kotu ya tambayi Bafulatanin da ke ikirarin mallakar tunkiyar ko yana son rantsewa kan ikirarin nasa ko kuwa zai nemi shawara. Bafulatanin ya nemi a ba shi lokaci domin shawara da ‘yan uwansa.
Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi
Bayan sun fita daga kotu, bangarorin biyu suka nemi sulhu, inda daga bisani Bafulatanin ya yarda da biyan duk kuɗaɗen da aka kashe wajen sayen tunkiyar da kuma wahalar da masu saye da dillalai suka sha, tare da mayar da tunkiyar ga wanda ya saya a kasuwar Kura.
Bayan an cimma matsaya, bangarorin suka koma gaban kotu, inda Insifekta Nasiru Dan-Sakkwato ya sanar da Alkalin kotu cewa sun yi sulhu.
Malam Naziru Abdullahi Tanburawa ya yaba da sulhun da aka cimma, inda ya bayyana cewa sulhu alkhairi ne a addinin Musulunci, sannan ya sallami bangarorin cikin lumana.