Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin a cire sunan Maryam Sanda daga cikin jerin mutanen da aka tsara za a yi wa afuwa .
Maryam Sanda dai ita ce wadda kotu ta yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya a shekarar 2020 bayan ta sameta da laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Haliru Bello.
Ta kai ƙarar zuwa kotun daukaka kara har zuwa kotun koli, amma a shekarar 2022 kotun koli ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke mata.

Majiya mai tushe ta tabbatar da cewa shugaban ƙasa ya bayar da umarnin a sake duba jerin sunayen wadanda ake son a yiwa afuwa domin tabbatar da cewa an cire waɗanda suka aikata manyan laifuka ba.
A cewar umarnin, an cire sunayen mutanen da aka tabbatar da aikata laifin kisa, garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi, safarar mutane, damfara, da kuma mallaka ko safarar makamai ba bisa ƙa’ida ba.
Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi
Haka zalika, Shugaba Tinubu ya amince da rage wa wasu daurarru hukunci – musamman wadanda aka ambata yi musu afuwar a baya ndomin rage cunkoson gidajen yari, tare da tabbatar da cewa gwamnati ba ta sassauta wa masu laifukan tashin hankali da manyan laifuka ba.
Wannan mataki, a cewar fadar shugaban ƙasa, na daga cikin tsarin gyaran shari’a da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa, wanda ya haɗa tausayi da adalci da kuma tabbatar da tsaron jama’a.