Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga dukkan wakilai daga arewacin Nigeria da su ɗauki matakin gaggawa don ganin an soke ɗaukar aikin kwastam da aka yi a kwanan nan.
A yayin zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin Kakakin majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, ’yan majalisar sun nuna ɓacin rai kan yadda aka gudanar da aikin ɗaukar ma’aikatan, suna kiran shi da Wanda yake cike da son kai da rashin adalci.
Majalisar ta ce “Duk da yawan al’ummar Arewacin Najeriya, an nuna bambanci mai yawa wanda ya saɓa wa ƙa’idojin hukumar rabon muƙamai ta ƙasa.”

Shugaban masu rinjaye a majalisar, Hon. Lawal Hussain Dala, wanda ya gabatar da ƙudurin, ya ce “Tsarin bai kasance mai gaskiya ba, kuma akwai rashin daidaito da rarrabuwar kawuna da nuna bambanci.”
Ya ce “Lissafin da aka fitar ya nuna fifiko ga yankin kudu musamman yankin kudu maso yamma, abin da ta bayyana da abin takaici da haɗari ga haɗin kan ƙasa.”
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin sabbin jami’an kwastam 1,785 da aka ɗauka, fiye da 1,000 daga cikinsu sun fito ne daga yankin Kudu, yayin da yankin arewa bai samu fiye da mutum 540 ba.
Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi
Majalisar Kano ta zargi hukumar kwastam da nuna fifiko ga yanki ɗaya kawai da nuna rashin gaskiya da nuna wariya.
A yayin da yake jagorantar zaman, Falgore, ya buƙaci wakilan arewa a majalisar tarayya da su sa baki don dakatar da wannan ɗaukar aikin.
Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa da ya soke jerin sunan ma’aikatan gaba ɗaya saboda rashin daidaitonsa.