Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahoton da Cibiyar Wale Soyinka ta fitar, wanda ya zargi gwamnatin jihar da take ‘yancin faɗin albarkacin baki ga ‘yan jarida a jihar .
A wata tattaunawa da manema labarai, Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana rahoton a matsayin “mara tushe balle makama,” inda ya ce gwamnatin Kano tana mutunta ‘yancin ‘yan jarida bisa doka da tsarin mulkin ƙasa.
“Gwamnatinmu tana maraba da kowace irin suka muddin an gina ta bisa gaskiya da hujjoji. Amma ba za mu lamunci kirkirarren labari ba wanda manufarsa ita ce bata sunan gwamnati,” in ji Waiya.

Kwamishinan ya kara da cewa, gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ci gaba da tabbatar da mulkin dimokuraɗiyya da kare ‘yancin ‘yan jarida da kungiyoyin farar hula.
Idan za a iya tunawa, a cikin rahoton Cibiyar Wale Soyinka mai taken “Shrinking Freedoms: 2024 Journalism and Civic Space Status Report”, an ambaci Jihar Kano a matsayin daya daga cikin jihohin da aka fi samun rahotannin take ‘yancin faɗin albarkacin baki na ‘yan jarida tare da jihohin Lagos da Abuja.
Sai dai a martanin sa, Kwamishina Waiya ya ce, “Rahoton ba shi da madogara, kuma an fitar da shi ne da wata manufa ta siyasa. Cibiyar ma bata da wakilai a jihohin Najeriya da ke tattara sahihan bayanai musamman a Kano.”
Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Wadanda Za a Yi Wa Afuwa
Ya kuma bayyana cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu lambobin yabo da dama daga manyan jaridun ƙasar saboda kyakkyawar hulɗarsa da manema labarai. Daga cikin su har da Leadership Newspaper, wacce ta karrama shi da matsayin Gwamnan da Ya Fice Wajen Cigaban Ilimi a Najeriya, da kuma African Leadership Magazine, wacce ta ba shi lambar yabo ta “African Governor of the Year for Good Governance.”
Waiya ya ce, “Wannan yana tabbatar da cewa Kano tana cikin jerin jihohi da ke mutunta aikin jarida a Najeriya. Hakan ne ma ya sa jaridun ƙasa ke ganin Gwamna Yusuf a matsayin shugaba mai karɓar ra’ayi da buɗaɗɗen tunani.”
A ƙarshe, Kwamishinan ya kawo misalin yadda Gwamna Yusuf ya karɓi masu zanga-zangar adawa da rashin kyakkyawar gwamnati a shekarar 2024 cikin lumana, yana mai cewa, “Shi ne kaɗai gwamna a Najeriya da ya karɓi masu zanga-zangar da kyakkyawar niyya, domin gwamnatinsa tana bude kofarta ga jama’a.”