Shugaban Karamar Hukumar Ungogo, Hon. Tijjani Amiru Bilyaminu Rangaza, ya raba na’uarori masu kwakwalwa (kwamfutoci) ga dalibai goma sha biyu ‘yan asalin Ungogo da Gwamnatin Jihar Kano ta ba su tallafin karatun digiri na biyu (Master’s Degree) a kasar Indiya.
An gudanar da bikin bayar da kayan a harabar sakatariyar karamar hukumar, inda Hon. Rangaza ya shawarci daliban da su kasance jakadun Ungogo na gari tare da mayar da hankali kan karatunsu.

Ya jaddada cewa ilimi shi ne ginshikin ci gaban kowace al’umma, don haka karamar hukumar ta yanke shawarar tallafa musu da kwamfutoci domin sauƙaƙa musu karatu da kuma karfafar su wajen amfani da sabbin hanyoyin karatu na zamani.
Shugaban ya yi musu fatan alheri, tare da addu’ar Allah ya basu nasara da dawowa lafiya.
Shugaba Tinubu ya nemi Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na yankin Usman Muhammad Kabir ya sanyawa hannu , ya ce Wasu daga cikin daliban da suka amfana, Jibrin Musa Uba da Kabiru Auwal Sale, sun bayyana farin cikinsu tare da godewa shugaban bisa wannan kyauta, suna mai alkawarin yin amfani da kwamfutocin yadda ya kamata wajen karatun su.
Bikin ya gudana a sakatariyar Karamar Hukumar Ungogo, inda manyan baki da suka halarta suka haɗa da shugabannin siyasa, kansiloli, iyaye da sauran jama’a.