Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya aika wa Majalisar Dattawan Nigeria da buƙatar tabbatar da sabbin hafsoshin tsaro da ya naɗa kwanan nan.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasiƙar shugaban ƙasa yayin zaman majalisar na ranar Talata.

A cikin jerin sabbin hafsoshin, Tinubu ya naɗa Manjo Janar Olufemi Oluyede a matsayin Babban Hafsan Tsaro, Manjo Janar Waheedi Shaibu a matsayin Babban Hafsan Sojojin Ƙasa, Rear Admiral Idi Abbas a matsayin Babban Hafsan Rundunar Sojan Ruwa, Air Vice Marshal Kennedy Aneke a matsayin Babban Hafsan Sojan Sama, da kuma Manjo Janar Emmanuel Undiendeye a matsayin Daraktan Tsaron Sirri na Ƙasa.
INEC ta ce ta kammala shirye-shiryen zaben gwamna na Anambra
A cikin wasiƙarsa, Shugaba Tinubu ya roƙi majalisar da ta hanzarta tabbatar da waɗannan naɗe-naɗe, domin a cewarsa, hakan zai taimaka wajen inganta gyaran tsaro da gwamnatinsa ke aiwatarwa tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro wajen yaƙi da ta’addanci, ‘yan bindiga da sauran barazanar tsaro.
Majalisar ta tura buƙatar shugaban ƙasa zuwa wani kwamiti domin gudanar da tantancewa da tabbatarwa, wanda za a gudanar a ranar Laraba.