INEC ta ce ta kammala shirye-shiryen zaben gwamna na Anambra

Date:

Shugaban Hukumar Zabe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya tabbatar da cewa hukumar ta kammala dukkan shirye-shiryenta domin gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra da za a yi ranar 8 ga Nuwamba, 2025.

Yayin taron kwamitin hadin gwiwa na tsaro kan zaben da aka gudanar a Abuja, Farfesa Amupitan ya ce hukumar ta za ta tura ma’aikata 24,000 a rumfunan zabe 5,718. Ya kara da cewa za a tattara sakamakon a matakan mazabu 326, kananan hukumomi 21 da kuma cibiyar tattara sakamakon zabe ta jihar da ke Awka.

Ya bayyana cewa hukumar ta tsawaita lokacin karɓar katin zabe zabe (PVC) daga 29 ga Oktoba zuwa 2 ga Nuwamba bayan gano cewa kashi 63.9 cikin 100 ne kawai su ka karɓi katin nasu.

FB IMG 1753738820016
Talla

Farfesa Amupitan ya ce an tanadi motocin haya 200 da jiragen ruwa 83 don jigilar ma’aikata da kayan zabe, tare da jaddada cewa hukumar za ta tabbatar da gudanar da sahihin zabe mai inganci. Ya kuma gargadi masu sayen kuri’a da cewa jami’an tsaro ba za su lamunci irin wannan dabi’a ba.

Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro na ƙasa (NSA), Mallam Nuhu Ribadu, ta bakin Daraktan Tsaron Cikin Gida, Hassan Abdullahi, ya tabbatar da cewa gwamnati ta tanadi matakan tsaro don tabbatar da zaman lafiya a lokacin zaben.

Maikwatashi: Tsohon kwamishinan Ilimi ya rubutawa gwamnan Kano budaddiyar Wasika

Shugaban Hukumar NYSC, Janar Olakunle Nafiu, ya tabbatar da cewa an tanadi tsaro da walwala ga dukkan matasa masu yiwa Kasa hidima da za su yi aiki a lokacin zaben. Ya ce za su yi aiki tare da INEC da jami’an tsaro wajen kare lafiyar su, inda ya bukaci al’ummar Anambra su kula da su kamar ’ya’yansu.

A nasa bangaren, Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya ce an tura jami’an yansanda 45,000 a fadin jihar don tabbatar da tsaro kafin, lokacin da kuma bayan zaben.

Ya ce jami’an tsaro na gwamnatin tarayya ne kawai za su yi aikin zaben, inda ya hana duk wata kungiya ta sa kai shiga harkar zabe. Ya kuma tabbatar da cewa za a sanya dokar takaita zirga-zirga a ranar zabe don tabbatar da tsaro da daidaito.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu Ya Cire Maryam Sanda Daga Jerin Wadanda Za a Yi Wa Afuwa

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya bada umarnin a...

Majalisar Kano ta buƙaci a soke ɗaukar aikin kwastam da aka yi a kwanan nan

Majalisar dokokin jihar Kano ta yi kira ga dukkan...

‎ ‎Kuskure ne Tinubu ya cigaba da ciyo wa Nigeria bashi bayan ya cire tallafin mai – Sarki Sanusi

‎ ‎ ‎Sarkin Kano kuma tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN),...

Shugaban Karamar Hukumar Ungogo Ya Raba Kwamfutoci Ga Daliban da Suka Samu Tallafin Karatu Zuwa Kasar Indiya

Shugaban Karamar Hukumar Ungogo, Hon. Tijjani Amiru Bilyaminu Rangaza,...