Ba mu da wata matsala da Ofishin mataimakin shugaban Kasa – NAHCON

Date:

Hukumar Alhazai ta kasa (NAHCON) ta karyata wani rahoto da jaridar News Point Nigeria ta wallafa da ke zargin shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, da amfani da hukumar tsaro ta DSS wajen tsare editan jaridar saboda wai ya fallasa zarge-zargen rashawa.

A wata sanarwa da ofishin shugaban hukumar ya fitar, NAHCON ta bayyana labarin a matsayin ƙarya, dake cike da ɓatanci da nufin ɓata suna.

Hukumar ta ce Farfesa Abdullah Usman bai taba bayar da umarni ko neman kama wani ɗan jarida ba, tare da kalubalantar jaridar da ta gabatar da hujja kan zargin.

Kashim Shattima ya sauka daga kujerar ta mataimakin shugaban Nigeria ya baiwa wata yarinya

NAHCON ta kuma bayyana cewa zarge-zargen rashawa da jaridar ta maimaita tsofaffin ikirari ne marasa tushe, tana mai cewa hukumar tana aiki cikin gaskiya da bin ka’ida.

Sanarwar ta ƙara da cewa, hukumar na da kyakkyawar alaƙa da ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, sabanin yadda rahoton ya nuna.

NAHCON ta yi kira ga jama’a da su yi watsi da rahoton, tana mai cewa jaridar ta daɗe tana yada labaran ƙarya da nufin ɓata sunan Shugaban hukumar NAHCON.

A cewar sanarwar, hukumar za ta ci gaba da ba kafafen yada labarai haɗin kai, amma ba za ta yarda da ɓatanci da ƙirƙirar karya ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya nemi hukumar NBC ta fadada aikinta kan kafafen yada labarai na intanet

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci Hukumar...

RMK@69: Kwankwaso Jagora Ne Mai Hangen Nesa, Abba Kuma Na Kawo Ci Gaba a Kano – Bakwana

Wani jigo a kungiyar Kwankwasiyya, kuma tsohon mai ba...

Da dumi-dumi: Tinubu ya nada sabon Minista

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunan...

Kashim Shattima ya sauka daga kujerar ta mataimakin shugaban Nigeria ya baiwa wata yarinya

Mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima ya sauka daga kujerarsa...