Wani jigo a kungiyar Kwankwasiyya, kuma tsohon mai ba da shawara ga gwamnan Kano, Alhaji Mustapha Hamza Buhari Bakwana, ya bayyana tsohon gwamnan jihar Kano, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, a matsayin jagora mai hangen nesa wanda burinsa a koyaushe shi ne inganta yankin Arewa da Najeriya baki ɗaya.
Bakwana ya bayyana hakan ne a cikin sakonsa na ta Jagora Kwankwaso murnar cika shekaru 69 da haihuwa a ranar Talata.
A cewarsa, Kwankwaso wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP kuma dan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023 jajirtacce ne mai kishin al’umma, wanda ya yi fice wajen ilimi da kiwon lafiya, inda ayyukansa suka sauya rayuwar mutane da dama a Kano da ma Najeriya baki ɗaya.
“A yau muna taya murna ga shugaba mai hangen nesa, wanda burinsa shi ne ci gaban jama’a da ɗaukaka kasar nan. Allah ya ƙara masa lafiya da nasara, ya kuma tabbatar mana da ganin manufofinsa sun tabbata,” in ji Bakwana.
Kashim Shattima ya sauka daga kujerar ta mataimakin shugaban Nigeria ya baiwa wata yarinya
Ya ƙara da cewa yana da tabbacin cewa salon jagorancin gwamnan jihar Kano na yanzu, Injiniya Abba Kabir Yusuf, zai ɗora a kan tubalin da aka kafa wajen bunkasa Kano zuwa babban birni mai kyan gani da ci gaba.
“Gwamna Abba yana tafiya da sahihiyar manufa ta jagorancin Jagora Kwankwaso wacce ke nufin raya Kano da tabbatar da jin daɗin jama’a. Tabbas, ayyukan da ake gani yanzu za su sauya fasalin jihar,” in ji shi.
Bakwana ya kammala da addu’ar Allah ya ba Injiniya Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso tsawon rai, lafiya, da albarka, yana mai jaddada cewa shugabancinsa zai ci gaba da zaburar da al’umma zuwa ci gaba da haɗin kai.