Mataimakin shugaban Kasa Kashim Shattima ya sauka daga kujerarsa ,inda ya baiwa wata yarinya ta hau kujerar na wucin gadi.
A jiya, a fadar shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya gana da tawagar PLAN International ƙarƙashin jagorancin Helen Mfonobong Idiong, daraktar shirye-shirye da kirkire-kirkire ta ƙungiyar.
A yayin ziyarar, Shettima ya bai wa wata yarinya mai suna Joy Ogah damar zama mataimakin shugaban ƙasa na wucin gadi, inda ta yi jawabi ga al’umma.
Yayin da yake jawabi a wajen taron, Mataimakin Shugaban Ƙasa ya tabbatar wa masu ruwa da tsaki da sauran al’umma cewa, Shugaba Bola Ahmad Tinubu na da cikakken ƙuduri wajen inganta ilimin ’ya’ya mata a fadin Najeriya.
RMK@69: Tinubu ya yi wa Kwankwaso kyakykyawan yabo
Ya ce, daga cikin manufofin gwamnati na tallafa wa ilimin ’ya’ya mata, shirin ciyar da ɗalibai a makarantu na daga cikin muhimman matakai da ake aiwatarwa.
Haka kuma, ya bayyana Uwargidan Shugaban Ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, a matsayin wacce ya kamata a rika koyi da ita , saboda yadda take taimakom ya’ya mata domin su zamo masu dogaro da kanwunansu.