A wani yanayi na al’ajabi, Kungiyar Kwallon Kafa ta Barau FC ta doke abokiyar burmin ta, Kano Pillars 2-1 a wasan mako na 9 na Gasar Firimiya ta Ƙasa (NPFL).
Barau FC ta bada mamaki ne bayan da ta farke kwallon da Pillars ta jefa mata sannan ta ƙara a wasan hamayya na farko a tarihi tsakanin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafan biyu da ke gari ɗaya.
Tun a minti na 20 da take wasan Rabi’u Ali ya ci wa Kano Pillars, Amma a minti na 52, Abdulbari Nura ya farke, inda daga bisani Stanley Oganbor ya ƙara, lamarin da ya jefa yan wasan kungiyar cikin murna da farin ciki.
Da ya ke tsokaci kan wasan, Shugaban kungiyar Barau FC, Shawall Barau Jibrin ya ce nasarar ta nuna irin ƙwazon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin wajen kafa ƙungiyar ƙwallon ƙafa da za a gafarta da ita a fadin ƙasar.
Ya ce nasarar ta nuna cewa lallai Barau FC za ta iya karawa a ko wanne matakin kwallon a Nijeriya.