Shugabancin ƙungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ya sanar da dakatar da Mai horas da ƴan wasa na ƙungiyar, Ogenyi Evans, da Babban Kocin ta, Ahmed Garba (Yaro Yaro), nan take, sakamakon rashin gamsasshen sakamakon da ƙungiyar ke samu a kakar gasar Firemiya ta ƙasa .
Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da Sashen Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na ƙungiyar ya fitar a jiya Lahadi, inda shugabancin kungiyar ya bayyana damuwarta kan yadda ƙungiyar ke samun sakamako maras kyau.
Pillars ta buga wasanni 8 zuwa yanzu, inda ta samu nasara a wasanni 2 kacal, ta yi kunnen doki 2 sannan ta sha kashi a wasanni 4.
“Wannan mataki ya zama dole sakamakon yadda ƙungiyar ke yin wasanni marasa kyau wanda bai dace da tsammanin hukumar gudanarwa da magoya bayan ƙungiyar ba,” in ji sanarwar.
A halin yanzu, tsohon kyaftin ɗin ƙungiyar kuma Mataimakin Koci, Gambo Muhammad, zai jagoranci harkokin horo na ƙungiyar na ɗan lokaci. Zai yi aiki tare da Kocin masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu.
Ƙungiyar Kano Pillars, wadda aka fi sani da Sai Masu Gida, na fatan wannan sauyi zai taimaka wajen farfaɗo da ƙungiyar a ci gaba da kakar gasar NPFL.