Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula da aikin hajji ta Ƙasa (NAHCON) da ta sake rage kuɗin aikin Hajjin shekara ta 2026 ba tare da bata lokaci ba.
Umarni ya fito ne bayan wani taro da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa da shugabanin hukumar NAHCON, inda Sanata Ibrahim Hadeija, mataimakin shugaban ma’aikata na fadar shugaban ƙasa, ya bayyana cewa shugaba Tinubu bai gamsu da farashin da aka bayyana a baya ba.
A baya dai, hukumar NAHCON ta bayyana kuɗin aikin Hajji kamar haka:
Masu tafiya daga yankin Maiduguri da Yola za su biya kusan naira miliyan 8 da dubu dari 3
Masu tafiya daga sauran jihohin Arewa za su biya kusan naira miliyan 8 da dubu dari 2.
Yayin da masu tafiya daga jihohin Kudanci za su biya kusan naira miliyan 8 da dubu dari 5.
Tinubu ya ce wadannan farashin sun dogara ne da canjin dala a naira 1,550, wanda ya kira da “matakin da bai daidaita da halin yanzu ba,” la’akari da yadda darajar Naira ta fara karuwa a kasuwa.
Ya bayyana cewa idan aka sake lissafi bisa sabon canjin dala, za a iya rage kuɗin zuwa tsakanin naira miliyan 7.6 zuwa 7.7, domin sauƙaƙa wa maniyyata da ke shirin zuwa aikin Hajji na shekarar 2026.
Haka kuma, hukumar NAHCON ta ce ta samu rangwamen kuɗi na naira biliyan 19 daga masu ba da sabis a ƙasar Saudiyya, wanda hakan ya taimaka wajen rage wasu daga cikin kuɗaɗen tafiya.
Bayan wannan, rahotanni daga wasu kafafen labarai sun nuna cewa hukumar ta sanar da sabon farashi da aka rage da naira dubu 200,000 daga wanda aka fara bayyana.
Masana sun bayyana cewa kuɗin aikin Hajji yana da alaƙa kai tsaye da canjin kuɗi tsakanin Naira da Dala, da kuma yadda ake biyan kuɗaɗen sabis a Saudiyya, don haka duk lokacin da Naira ta ƙara ƙarfi, ana iya rage farashin tafiyar.
Sai dai wasu kwararru sun nuna damuwa cewa duk da wannan ragewa, NAHCON ba ta da faɗin da za ta yi manyan sauye-sauye, saboda yawancin kwangiloli da aka kulla da masu samar da sabis a Saudiyya sun riga sun fara aiki.