Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Date:

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano , ta fara bincikar tsohon gwamnna Jljihar, Abdullahi Umar Ganduje, kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan huɗu zuwa aikin Dala Inland Dry Port.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa ana zargin kuɗin an kashe su wajen bayar da kwangila don samar da wasu abubuwan more rayuwa a wajen aikin.

An gano yadda aka mayar da kashi 20 na kuɗin wanda mallakar jihar ne zuwa ga iyalan Ganduje a shekarar 2020.

Wannan ya janyo an cire Jihar Kano daga cikin masu mamallaka kamfanin, inda ’ya’yan Ganduje ke riƙe da muƙamakn daraktoci da wasu masu hannun jari.

‎Yadda Sunan Ganduje ya bayyana a wata badakalar hannun jari ta gwamnatin Kano

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa binciken ya fara ne bayan hukumar ta samu koke-koke daga jama’a kan zargin karkatar da kuɗin.

Da yake tabbatar da lamarin, shugaban hukumar PCACC, Saidu Yahya, ya ce binciken zargin karkatar da kuɗin jihar ya kusa kammaluwa.

“Eh, mun samu koke-koke daga jama’a kan zargin karkatar da sama da Naira biliyan huɗu na kuɗin Jihar Kano zuwa Dala Inland Dry Port da tsohuwar gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ta yi,” in ji Yahya.

“Zuwa yanzu mun gayyaci wasu da ake zargi da hannu a lamarin. An kama mutum ɗaya, an yi masa tambayoyi, daga baya kuma an bayar da shi beli bayan ya bayar da muhimman bayanai.

“Bincike ya kuma gano cewa ɗaya daga cikin waɗanda ake zargi yanzu yana Yola, a Jihar Adamawa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa za a kai lamarin zuwa kotu nan ba da jimawa ba, domin binciken ya tabbatar da cewa akwai isassun hujojji don ci gaba da shari’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...

Sanata Barau zai raba Naira 20,000 ga mutane 10,000 a Jihar Kano

Mataimakin shugaban majalaisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibrin zai...