Ƙungiyar Forum of Progressive Academics ta Yi Allah-wadai da Yunkurin Siyasantar da Bikin Cikar Najeriya Shekara 65 a Kano

Date:

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta yi Allah-wadai da abin da ta kira yunƙurin siyasantar da bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai a Jihar Kano.

Da yake jawabi a taron manema labarai da aka gudanar a cibiyar yan jaridu ta NUJ ta Kano, shugaban ƙungiyar, Dr. Abubakar Isa Ibrahim, ya bayyana cewa sun ga wajibcin su fito fili su yi tir da yadda ake ƙara shigar da siyasa cikin harkokin tsaro a jihar, abin da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar jihar kano.

Dr. Ibrahim ya bayyana cewa shiyasa ce tasa aka janye jami’an ‘yan sanda daga faretin bikin ranar yancin Kan Nigeria a Kano, kuma akwai manufar da wasu ‘yan siyasa ke da ita ta neman tayar da hankali a Kano.

“Mun taru a nan domin nuna damuwarmu saboda yadda ake kokarin siyasantar da harkar tsaro a kano,” in ji shi.

Ƙungiyar ta bayyana rashin jin daɗinta kan wannan abin da ta kira nuna bambanci, tana mai cewa yayin da sauran jihohi suka gudanar da bukukuwansu tare da cikakken goyon bayan jami’an tsaro, Kano ce kaɗai ta zamo saniyar ware. “Wannan lamarin yana cutar da Kano,” in ji Dr. Ibrahim.

Ya ce wannan lamari ya shiga jerin abubuwan da aka yi na sanya siyasa cikin harkokin jihar, musamman yadda aka rika yi a sha’anin da ya shafi Masarautar kano a baya.

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

“Wasu marasa kishin ƙasa sun kuduri aniyar ganin Kano ta ci gaba da kasancewa cikin rikici don biyan bukatarsu ta siyasa,” in ji shi, yana mai gargadin cewa irin wannan dabi’a na iya lalata zaman lafiyar Kano .

Ƙungiyar ta kuma nuna damuwa kan rawar da kwamishinan ‘yan sanda na jihar ke takawa, inda ta zarge shi da hannu a cikin abin da ta kira makircin siyasa.

Kungiyar ta roƙi Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya saurari kiran Gwamna Yusuf na neman a gaggauta sauya Kwamishinan ‘Yan Sanda. “Wannan zai jawo jama’ar Kano su cigaba da amincewa hukumomin tsaro kuma ya nuna cewa gwamnatin tarayya na adalci,” in ji Dr. Ibrahim, yana mai jaddada cewa mutunta ikon jihohi abu ne da zai tabbatar da daidaito da zaman lafiya a ƙasa.

Ƙungiyar ta kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa juriya da kishinsa na tabbatar da gudanar da bikin cikar Najeriya shekaru 65 duk da kalubalen da ya fuskanta. “Duk mai kishin Kano da Najeriya dole ne ya yabawa jarumta da kishin gwamnan Kano ga al’umma,” in ji Dr. Ibrahim.

Taron manema labarai ya ƙare da kira ga dukkan masu ruwa da tsaki da su haɗa kai wajen kare mutunci da zaman lafiyar Jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Tinubu ya ba da Umarnin rage kudin aikin Hajjin 2026

Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya umarci hukumar kula...

Hukumar yaƙi da cin-hanci ta jihar Kano ta fara binciken Ganduje kan zargin karkatar da Naira biliyan 4 a Kano

Hukumar Karɓar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da...

Yan Uwa da Abokan Arzikin Sabon Kwamishinan Shari’a na Kano Sun Shirya masa addu’o’i na musamman

Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari'a na...

Sanata Barau zai raba Naira 20,000 ga mutane 10,000 a Jihar Kano

Mataimakin shugaban majalaisar dattawan Nigeria Sanata Barau Jibrin zai...