Yan uwa da abokan arziki na kwamishinan shari’a na jihar Kano Abdulkarim Maude SAN sun shirya masa saukar Alqur’ani mai girma da kuma addu’o’i na musamman domin ya sami nasarar fara aikin da gwamnan Kano ya dora masa .
Alarammomi da dama ne suka hadu da yan uwan sabon kwamishinan domin gudanar da addu’o’in a Unguwar Kwana hudu dake karamar hukumar Nasarawa inda Abdulkarim Maude ya tashi.
Da yake zanyawa da wakilin Kadaura24 bayan kammala sauka da addu’in Guda cikin makusantan sabon Kwamishinan mai suna Usman Abdu ya ce sun shirya taron addu’o’in ne domin nemawa Abdulkarim Maude SAN taimakon Allah a aikin da gwamnan Kano ya ba shi.
” Nan da ka ke gani yan uwa ne da abokan arziki da su ka tashi tare da sabon Kwamishinan Shari’a su ka hadu domin yi masa addu’o’i na musamman bayan saukar Alqur’ani mai girma don nema masa Allah ya Bashir nasarar sauke nauyin da gwamnan ya dora masa”. A cewar Usman Abdu
Ya ce dama kwamishinan ya saba shirya Irin wadannan addu’o’i ga Gwamnan Kano musamman lokacin da ake shari’a da kuma lokacin da yake yakin neman zabe, haka ta sa muma yanzu muka shirya masa don ganin ya sami taimakon Allah Madaukakin Sarki .
” Muna da kwarin gwiwar Abdulkarim Maude zai yi aiki tsani da Allah kuma zai yi abun da bama a tsammani daga gare shi, saboda kwararren lauya ne kuma mutum ne mai taimakon mutane , don haka muka baiwa gwamnan Kano tabbacin Abdulkarim ba zai ba shi kunya ba”. Inji Usman Abdu
Usman Abdu ya ce sun alkawarin cigaba da shiryawa Kwamishinan shari’a na jihar Kano Irin wadannan addu’o’i na musamman domin ya sami nasarar a aikin da gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya dora masa