Majalisar wakilai ta wakilai ta ce ta na duba yiwuwar gudanar da zaben shugaban ƙasa, gwamna da kuma na majalisun dokoki a rana ɗaya, a wani yunkuri na sauya tsarin zabe a ƙasar nan.
Shugaban majalisar, Hon. Tajudeen Abbas, ne ya bayyana haka a lokacin da ya karɓi tawagar wakilai daga Tarayyar Turai (EU) a Abuja, inda ya ce matakin zai inganta sahihancin zabe, rage kashe kudade, da kuma ƙara yawan masu kada kuri’a a gaba.
Abbas ya ce gudanar da dukkan zabe a rana guda maimakon yin su a ranaku daban-daban kamar yadda ake yi a yanzu, zai taimaka wajen kawar da ƙalubalen tsaro da matsalar rashin fitowar masu zabe.
Masu goyon bayan wannan kudiri sun bayyana cewa zai rage kashe kudade da rage hayaniya ta siyasa, ƙara yawan masu kada kuri’a da kuma rage matsalolin tsaro da ake fuskanta a lokutan zabubbuka.
Haka zalika, shugaban majalisar ya bayyana cewa akwai wasu sauye-sauyen da ake son a kundin tsarin mulki, ciki har da samar da kujeru na musamman ga mata da masu buƙata ta musamman, bayar da ’yancin kuɗi ga sarakunan gargajiya tare da fayyace rawar da za su taka, da kuma batun gudanar da dukkan manyan zabuka a rana guda.