Tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya tsunduma cikin wata badakalar harkallar biliyoyin naira da ya karkatar zuwa wani kamfani mallakar ƴaƴansa, wanda ya kamata wannan hannun jari na kaso 20 cikin 100 na gwamnatin jihar Kano ne.
A binciken kwakwaf da PREMIUM TIMES ta yi ta gano cewa kason gwamnatin Kano a tashar sauke kaya na Dala Ganduje ya karkatar da kashi 20 cikin 100 na kason gwamnatin Kano zuwa wani kamfani mai zaman kansa wanda mallakin ƴaƴan sa ne kamar yadda bincike ya nuna.
Kuma an bankado cewa ita wannan harkallar sai da ya saka ‘ya’ƴansa a cikin wannan kamfani tun da farko kafin ya mika wa kamfanin ƴaƴansa wannan kaso, ita jihar kuma sai da ta ji a salansa.
Hakan ya cire Jihar Kano daga zama mai hannun jari a aiki gaba ɗaya, ya kuma sanya ‘ya’yansa su zama daraktoci da masu wannan hannun jari. Haka kuma ba da jimawa ba Ganduje wanda a lokacin sa ne gwamna, ya ba da kwangilar ayyuka da asali gwamnatin jiha ce ke da alhakin aiwatarwa bisa yarjejeniyar da ka kulla tun farko.
Yadda Kano ta samu kaso a tashar sauke kaya ta Dala
A ranar 4 ga Satumba 2006, kusan shekara goma kafin Ganduje ya hau mulki, Gwamnatin Jihar Kano ta sayi kaso 20 cikin 100 a tashar (Dala Inland Dry Port Limited) a lokacin gwamnatin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.
Kwamishinan kasuwanci, masana’antu da haɗin gwiwa na Shekarau, Ahmad Yakasai, ya sanya hannu a yarjejeniyar a wancan lokaci.
Wannan mallaka da jihar Kano ta yi a lokacin ya biyo bayan manufar ci gaban tashoshin sauke kaya da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar a shekarar 2003, wadda ta karfafa gwiwar Kamfanoni masu zaman kansu su gina tashoshin, yayin da gwamnatin tarayya da jihohin masaukin tashar za su rika samun kaso kaɗan na hannun jari.
Wannan yarjejeniya ta gindaya cewa masu kamfanoni masu zaman kansu ba za su samu kason da ya wuce 60 cikin 100 ba, yayin da aka ware kaso 20 cikin 100 ga gwamnatin tarayya da wani kason 20 cikin 100 ga gwamnatin jiha.
Har ila yau wannan yarjejeniya ta kuma tanadi cewa gwamnati za ta ba da tashoshin da ta riga ta gina ga kamfanoni masu zaman kansu haya na shekaru 15 zuwa 25, gwargwadon kayan aiki da aka girke. Idan kuma kamfanonin ne suka gina tashar tun farko, tsarin ta fayyace cewa kaso na gwamnatin tarayya da na jiha zai kasance kalilan ne.
Tashar Sauke kaya ta ‘Dala Inland Dry Port’
Tashar Dala Inland Dry Port na da matukar muhimmancin gaske a Kano, cibiyar kasuwanci ta Arewacin Najeriya. An ƙirƙire ta ne domin sauƙaƙa shigowa da fitar da kaya, rage lokacin jigilar su, da kuma inganta cinikayya da ƙasashen makwabta marasa gabar teku kamar Nijar, Chadi da Kamaru.
Bisa ga wasu muhimmin takardu da PREMIUM TIMES ta mallaka, Jihar Kano ta ɗauki alhakin biyan kaso 20 cikin 100 na hannun jarinta ta hanyar samar da ababen more rayuwa, wato hanyoyi, shinge, wutar lantarki da ruwa a wurin aikin Zawachiki da ke karamar hukumar Kumbotso ta jihar.
Sai dai, tsohon gwamna Shekarau, wanda ya yi wa’adin mulki biyu a jere daga 2003 zuwa 2011, bai aiwatar da wani aiki ba a tashar.
Haka shima magajinsa, Rabiu Kwankwaso, wanda wa’adinsa na biyu da ba a jere ba ya ƙare a 2015, shi ma bai waiwayi tashar ba kwatakwata.
PREMIUM TIMES ta gano cewa, bayan Ganduje a lokacin ya na gwamna, saka ‘ya’yansa a cikin kamfanin da za su mallaki wannan tasha, sai ya zaftari kudin jihar sar sama da naira biliyan 2 ya bada kwangilar a gyara wanna tasa domin ta soma aiki. Yayi amfani da ikonsa na gwamna a wancan lokacin in da ya yi gaban kasa ya maika kason jihar ba tare da bin doka da ka’ida ba zuwa ga wannan kamfani da ya’yansa ke da mallaki.
Babban darektan ma’akatar kasuwanci da cinikayya ta jihar Kano Bashir Uba, ya shaida wa PREMIUM TIMES cewa lallai jihar Kano bata saida wa kowa hannun jarinta na tashar dala ba. Hasali ma a yanzu haka ta binciken yadda aka yi wasu da ba gwamnati ba ke da mallakin kashi 80 na hannun jarin wannan tasha.
” Gwamnatin Kano ta na shirin kara jarinta a wannan tasha, amma kuma dole za ta gudanar da bincike kan badakalar da ya cukuikuye masu mallakar wannan tasha a yanzu.
PREMIUM TIMES ta ziyarci wannan tasha ta iske ana tafka hadahada ta kasuwanci matuka, sai dai kuma ga yadda lamarin yake jihar Kano bata mafana da komai a wannan tasha.