Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Kebbi, ta bayyana rashin amincewarta da cire kimanin naira miliyan 14 (₦14,000,000) daga albashin malamai a watan Satumba na shekarar 2025.
Shugaban NLC na jihar, Comrade Murtala Usman, ya bayyana hakan yayin da yake karin haske kan rahoton da ya fito daga Ƙungiyar Malamai ta Ƙasa (NUT), inda aka nuna cewa an cire kuɗin ba tare da sahalewar malamai ko wata doka ba.
A cewarsa, “Mun kafa kwamitin bincike domin tantance gaskiyar al’amarin, kuma kwamitin ya tabbatar da cewa an cire kuɗin ba bisa ƙa’ida ba.”
Binciken da aka gudanar ya bayyana cewa an cire kuɗin ne don biyan rajistar ƙwararru a Hukumar Teachers Registration Council of Nigeria (TRCN), amma babu wani bayani ko takarda da ke nuna cewa an nemi izini daga ofishin Gwamna ko na Kungiyar Malaman kafin wannan mataki.
Tawagar NLC ƙarƙashin jagorancin Comrade Murtala Usman ta gana da Ma’aikatun Ilimi da Na Kuɗi, sannan daga bisani ta gana da Mai Girma Gwamnan Jihar Kebbi. “A wajen ganawar, gwamnan ya bayyana cewa ba a nemi izinin sa ba kafin cire kuɗin, kuma bai bada wata amincewa ba.
Gwamnan ya bayar da umarni kai tsaye cewa a maido da kuɗin da aka cire ba bisa ƙa’ida ba ga dukkan malamai da abin ya shafa cikin gaggawa.
Haka kuma, ya gargadi Ma’aikatar Kuɗi da sauran ma’aikatu da su guji yin irin waɗannan cire-cire daga albashin ma’aikata ba tare da izinin rubutaccen umarni daga ofishin Gwamna ba.
A nata bangaren, NLC ta miƙa godiya ga gwamnan bisa wannan matakin gaggawa da ya ɗauka, wanda ta ce ya hana yuwuwar tashe-tashen hankula a fannin ilimi da masana’antu a jihar.
A ƙarshe, Comrade Murtala Usman ya shawarci mambobin ƙungiyoyin kwadago da su rika bi hanyoyin doka wajen isar da ƙorafe-ƙorafensu, ta ofisoshin ƙungiyoyi, domin gujewa rudani.
Shi ma Sakatare na NUT a jihar, Comrade Gazali Hassan Macido, ya nuna bacin ransa da yadda Ma’aikatun Ilimi da Na Kuɗi suka yi wannan cire kuɗi ba tare da tuntuɓar ƙungiyar malamai ba, yana mai kiran a rika yin abubuwa cikin shawarwari da fahimta.