Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya isa birnin Lagos a ranar Juma’a domin ziyarar aiki , yayin da Najeriya ke shirin bikin cikar ta shekaru 65 da samun ‘yancin kai a cikin salo na takaita bikin
Shugaban Ƙasan ya je Lagos ne bayan halartar bikin nadin Sarkin Ibadan, Oba Rashidi Ladoja, a tsohon birnin Ibadan dake jihar Oyo.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Kasar Bayo Onanuga ya fitar .
Yace a yayin zamansa a Lagos, Shugaba Tinubu zai gana da manyan ‘yan kasuwa na ƙasar da kuma jami’an gwamnati na matakin koli.
Kazalika, a ranar Talata 30 ga Satumba, Shugaban Ƙasan zai ziyarci jihar Imo domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka da Gwamna Hope Uzodimma ya aiwatar.
A cikin shagulgulan bikin ‘yancin kai, Shugaba Tinubu zai kuma kaddamar da sabuwar cibiyar al’adu da fasaha wadda aka chanza mata suna zuwa Cibiyar Wole Soyinka ta Al’adu da Fasaha.