Kungiyar Lauyoyin yan Asalin Jihar Kano ta Ƙasa ta aikawa Shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Majalisar Wakilai ta kasa takardun ƙorafi, tana neman a ci gaba da bincike kan Hon. Alhasan Ado Doguwa bisa zargin hannu a kisan da aka yiwa mutane a Tudun Wada yayin zaɓen 2023.
Lauyoyin sun bayyana cewa lamarin ya janyo mutuwar mutane da dama, don haka su ke kira ga Majalisar Ƙasa da ta saka baki domin tabbatar da adalci ga iyalan wadanda abin ya shafa.
Kungiyar ta roƙi kwamitocin Shari’a, ‘Yan Sanda, da kare hakkokin Dan Adam su shiga cikin binciken, domin samar da adalci ga waɗanda suka rasa rayukansu da kuma wadanda suka ji raunuka.
Haka kuma, sun bukaci shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai da su shirya taron jin ra’ayin jama’a ko kuma su nemi cikakken rahoto daga rundunar ‘yan sanda ko Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano kan batun.
Gwamna Abba ya amince da a sake ɗaukar malaman lissafi a makaratun Kano
Kungiyar taja hankali da cewa a tsarin mulkin dimokuraɗiyya babu wani dayafi ƙarfin sharia Rashin yin adalci ko barin wannan zargi ya tafi ba tare da bincike mai zurfi ba haka take doka ne kuma zai lalata tsarin shari’a.
Lauyoyi sun gabatar da wanan takarda ne biyo bayan Kai takarda offishin kwamishinan sharia na kano da hotunan wadanda lamarin ya shafa don haka ne suka kawowa tagwayen majalisun wanan korafi don daukar mataki
A ƙarshe, lauya Dr. Jafar Sadik, wanda ya sanya hannu a madadin kungiyar yace yana fatan majalisun zasu bibiyi hakkin jama’ar