Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya sauyawa wasu kwamishinoni da ma’aikata gwamnati ma’aikatu

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da sauyawa wasu kwamishinoni ma’aikatu, sannan kuma an sauyawa wasu ma’aikatan gwamnati a wasu muhimman ma’aikatun jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya aikowa Kadaura24.

Ya ce matakin yana daga cikin kokarin gwamnati na kara karfafa shugabanci da inganta ayyukan gwamnati a fannoni daban-daban.

A cewar sanarwar, Kwamishinan Shari’a na jihar, Barista Haruna Isa Dederi, an mayar da shi zuwa Ma’aikatar Sufuri. Haka kuma,  Darakta a Ma’aikatar Shari’a, Barista Mustapha Nuruddeen Muhammad, an mayar da shi Ma’aikatar Muhalli a matsayin Babban Sakatare.

FB IMG 1753738820016
Talla

Kwamishinan Harkokin Jin Kai, wanda ya kasance mai rikon kwarya a Ma’aikatar Sufuri, zai koma ma’aikatarsa ta asali, wato ta Harkokin Jin Kai.

Gwamna Yusuf ya umurci dukkan jami’an da sauye-sauyen suka shafa da su mika ragamar ofisoshinsu ga manyan jami’an da ke cikin ma’aikatun kafin kammala aiki gobe Talata, 23 ga Satumba, 2025.

Ganduje bai bar min ko sisi a baitul malin Kano ba sai bashi –Gwamna Abba

Gwamnan ya jaddada kudirin gwamnatinsa na gaskiya, inganci da shugabanci nagari, tare da bukatar jami’an gwamnati su ba da hadin kai ga sabbin kwamishinonin domin gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...

Gwamnan Kano ya tura sunayen mutane biyu majalisar dokokin don nada su a mukaman Kwamishinoni

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika...

NLC Reshen Kebbi Ta Soki Cire Naira Miliyan 14 Daga Albashin Malamai

Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Kebbi, ta...