Tsohon Babban Sakataren yada labaran Gwamnan Kano, Malam Abba Anwar, ya bayyana cewa har yanzu bai taba nadamar yin aiki a karkashin tsohon Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ba.
A wani rubutu da ya wallafa, Anwar ya ce wannan bayani da ya fitar somin tabi ne cikin littafin tarihin rayuwarsa da zai fitar nan gaba.

Ya ce ya yi aiki da Ganduje tsawon shekaru shida, daga watan Fabrairu 2018 zuwa Mayu 2023, ba tare da wani katsewa ba, kuma ya koyi abubuwa masu tarin yawa daga gogewar tsohon gwamnan, musamman kan harkokin tsare-tsaren tsaro da shugabanci.
“Ban taba nadamar yin aiki karkashin gwamnatin Ganduje ba. Na samu damar koyon aikin yada labarai tare da harkokin siyasa. Ganduje ya ba ni cikakken goyon baya wajen gudanar da aikina ba tare da katsalandan daga wasu jiga-jigai ko ‘yan uwa ba,” in ji shi.
Abba Anwar ya ce ya shaida yadda tsohon gwamnan ya taka rawar gani wajen tabbatar da tsaro a Kano, har ma ya kirkiro abin da ya kira “Ganduje Model of Security System”.
Ya kara da cewa gina gadojin sama da sabbin asibitoci a masarautu hudu da aka kirkira, da Asibitin kula da masu cutar daji a Giginyu da sauran muhimman ayyuka sun kasance abin alfahari gare shi a lokacin da yake mai magana da yawun tsohon gwamnan.
Tsohon CPS din ya ce a matsayinsa na kwararren ɗan jarida, bai taba yin aiki da siyasa a tare ba sai dai ya fi mai da hankali wajen kare martabar aikin jarida da kuma kungiyar NUJ.
Anwar ya yi suka bisa yadda wasu daga cikin masu kula da harkokin yada labarai a wasu gwamnatoci ke aikata rashin kwarewa, musamman wajen rubuta sanarwar manema labarai, inda ya ce hakan na rage darajar aikin.
Ya bayyana cewa koda yake babu wata gwamnati da ta taba zama cikakkiya ba tare da kura-kurai ba tun daga kafuwar jihar Kano, amma shi bai taba fito da rubutu ko magana da ya zargi tsofaffin gwamnati da rashin nagarta ba, ciki kuwa har da gwamnatin Kwankwaso, Shekarau, ko ta shi Gandujen kansa.
“Na koyi aikin jarida ne a matsayin sana’a, ba a matsayin siyasa ko kungiyar ma’aikata ba. Rubuta na gaba zai bayyana gaskiyar wasu labarai wadanda jama’a basu sani ba,” in ji shi.