Hukumar gyaran hali da tarbiyya ta Kasa reshen jihar Kano ta ce kimanin fursunoni 68 a Jihar Kano ne suka ci jarabawar kammala sakandaire ta NECO ta shekarar 2025.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, fursunonin sun ce wannan nasarar ta kasance abin farin ciki gare su inda suka bayyana cewa hakan zai zama wata babbar dama wajen sauya rayuwarsu gaba ɗaya.
Hukumar ta bayyana cewa wannan nasara ta samu ne sakamakon tallafin gwamnatin Kano, wadda ta ɗauki nauyin ci gaban ilimin fursunonin.
Ni ban taba yunkurin neman mulkar Nigeria a Zango na uku ba – Obasanjo
“Wannan shiri ya yi daidai da dokar hukumar kula da fursunoni ta Najeriya ta 2019, wadda ke mai da hankali kan gyara da sake tarbiyyar fursunoni ta hanyar ilimi da horo na sana’o’i.” in ji sanarwar.
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙara jaddada aniyyarta ta samar da damammakin ilimi ga fursunoni domin ƙarfafa su su zama abin koyi nagari a cikin al’umma.

Wannan mataki na cikin shirin muradun shugaba Tinubu na ‘Renewed Hope’, wanda hukumomin ƙasar suka ce yana ƙunshe da inganta rayuwar duk ‘yan Najeriya cikin har da fursunoni.
Solacebase