Ganduje bai bar min ko sisi a baitul malin Kano ba sai bashi – Gwamna Abba

Date:

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta gaji asusun gwamnatin jihar babu ko sisi tare da bashin da ya kai kusan Naira 9,000 daga ɗaya cikin asusun bankunan jihar, wanda tsohuwar gwamnatin da ta gabata ta bari.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya aikowa Kadarau24.

Da yake jawabi yayin raba takardun ɗaukar aikin koyarwa na dindindin ga malamai 4,315 da suka yi aiki a matsayin BESDA, a ranar Alhamis a Kano, gwamnan ya ce tuni aka sauya wannan yanayi, inda yanzu gwamnati ke da biliyoyin naira a asusun ta.

Ya zargi gwamnatin da ta gabata da rashin gaskiya wajen tafiyar da harkokin kuɗi, inda ya ce ta ɗauki masu tattara haraji sama da 128 amma babu wani gagarumin aiki da aka gani daga gare su.

Kada Ka Rudar da Tarihi, Ba Ka Cikin Wadanda Suka Kafa APC – Alfindiki Ya Fadawa Kwankwaso

“Idan suna da hujja, su fito su nuna mana aikin da suka yi a Kano. Amma abin da suka yi shi ne sun cinye baitulmali har suka bar jihar a cikin bashi,” in ji Yusuf.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen inganta harkokin kuɗaɗe da kuma toshe hanyoyin zurarewar kuɗi domin farfaɗo da tattalin arzikin jihar.

FB IMG 1753738820016
Talla

“Mun sadaukarwa da jin daɗinmu domin tabbatar da cewa kuɗin Kano ya dawo hannun al’umma, ba hannun shugabanni ba. Wannan shi ne ginshiƙin tafiyarmu kuma ba za mu sassauta akan haka ba,” in ji shi.

Gwamna Yusuf ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannoni na ilimi, lafiya da inganta ababen more rayuwa tare da tabbatar da gaskiya da rikon amana duk da sukar da ake yi daga ‘yan adawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Hukumar jin daɗin alhazai ta Kano ta sanar da kuɗin aikin hajjin badi

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta amince...

Kudade: Ganduje ya caccaki Gwamnatin kano

Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma Tsohon shugaban jam’iyyar APC...

Gwamnan Kano ya tura sunayen mutane biyu majalisar dokokin don nada su a mukaman Kwamishinoni

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika...

NLC Reshen Kebbi Ta Soki Cire Naira Miliyan 14 Daga Albashin Malamai

Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) reshen Jihar Kebbi, ta...