Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince tare da mara baya ga kudirin doka da zai baiwa kananan hukumomi 44 na jihar cikakkiyar ‘yancin kai ta fuskar kuɗi da gudanarwa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu kuma ya aikowa Jaridar Kadaura24.
Ya ce, Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin zaman majalisar zartarwa ta 31 a Gidan Gwamnati, Kwankwasiyya City, inda aka amince a mika kudirin ga majalisar dokokin jihar domin yin nazari tare da amince wa.
Gwamnatin Kano ta nemi majalisar dokokin jihar ta haramta auren jinsi
Ya ce wannan mataki zai baiwa kananan hukumomi damar gudanar da harkokinsu kai tsaye, aiwatar da ayyuka cikin gaggawa, da kuma yanke hukunci bisa bukatun jama’a.

Gwamnan, ya kara da cewa wannan sauyi zai tabbatar da gaskiya, riƙon amana, da hanzarta ci gaban al’umma, tare da zurfafa dimokuraɗiyya a Kano.