Yin rijistar katin Zabe zata taimaki addinin musulunci da musulmai – Mal Usman Mai Dubun Isa

Date:

Shahararren mai yabon Manzon Allah (S A W) Malam Usman Muhammad Tahir Wanda aka fi sani da Mai dubun Isa ya bukaci Matasan jihar Kano da Nigeria baki daya da tabbatar sun je sun yi rijistar katin zabe, domin yin haka zai ba su damar zabar Shugabannin da suke da kishin addinin musulunci.

Malam Usman mai dubun Isa ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da yayi da Jaridar Kadaura24 a Kano .

Ya ce tabbas Matasa suna da rawar takawa a sha’anin da ya shafi zabe, don haka ya ce ya na da muhimmaci su fita domin su karbi katin zaben don zabar wadanda za su inganta rayuwarsu da harkokin addinin musulunci .

Tinubu y ba da umarnin sake Karya farashin kayan Abinci a Nigeria

“Wannan kasar ta mu Nigeria ta na yafiya ne akan addinai daban-daban don haka mu ke baiwa Matasa shawarar su je su karbi katin zabe ko dan idan lokacin zabe ya zo mu nuna cewa addninin musulunci shi ne kan gaba a yawan mabiya a Nigeria “. Inji Mai dubun Isa

Ya ce yin rijistar katin zaben ga matasa zai taimakawa addninin musulunci ta hanyar zabar Shugabannin da suke da kishin addinin musulunci da kuma kin zabar Shugabannin da ba su damu da harkokin addini ba.

Da yake magana game da bikin takutaha kuwa, Malam Usman Muhammad ya ce akwai bukatar hukumomin tsaro su sanya Idanu sosai domin ganin mutanen da su ke fitowa da makamai da kuma masu yin abubuwan da suka sabawa dokokin Kasa da na addinin musulunci ba su sami damar yin hakan ba.

FB IMG 1753738820016
Talla

Ya kuma ba da tabbacin cewa shi da jama’arsa za su fita a ranar asabar din nan domin yin zagayen takutaha ba tare da daukar makami ba, sannan ya ce suma za su taimakawa jami’an tsaro wajen tabbatar da an yi taron Lafiya an gama Lafiya.

Malam Usman Mai dubun Isa ya kuma baiwa gwamnan jihar Kano shawarar ya rika Sanya idanu kan dukkanin kungiyoyin addnini don tabbatar da su na tafiya akan ka’ida ta addinin , domin ya ce Allah sai ya tambaye gwamnan Amanar da ya ba shi a ranar gobe kiyama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

INEC ta yi Allah-wadai da masu yakin neman zabe tun kafin lokaci ya yi

Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ta yi Allah wadai...

Tinubu y ba da umarnin sake Karya farashin kayan Abinci a Nigeria

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa wani...

Jami’ar MAAUN Da Kwalejin Seneca ta Canada Sun Kulla Alaka Don Inganta Kwarewar Turanci da Samar da Damar Karatu Ga Dalibai A Duniya

  Gamayyar rukunin jami’o’in MAAUN ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwar...

Hasashe 6 da Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi kuma suka tabbata a siyasar Kano

‎ ‎ ‎ ‎Musa Iliyasu Kwankwaso na daga cikin fitattun ’yan siyasar...