Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bai wa wani kwamiti na majalisar zartarwar ta tarayya umarnin daukar karin matakai don rage farashin kayan abinci a fadin kasar nan.
Minista a Ma’aikatar Noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ne ya bayyana haka a Abuja ranar Laraba.
Sanata Abdullahi ya bayyana cewa za a aiwatar da wannan umarni ta hanyar tabbatar da tsaro domin wucewa da kayayyakin amfanin gona da sauran kayan abinci cikin kwanciyar hankali a kan manyan hanyoyi a duk fadin Najeriya.
Hasashe 6 da Musa Iliyasu Kwankwaso ya yi kuma suka tabbata a siyasar Kano
Ya kara da cewa wannan mataki na daga cikin hangen nesa na shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu wajen cimma manufar sauko da kayan abinci mai dorewa a kasar.

Ministan ya jaddada cewa kwamiti na majalisar zartarwa na ci gaba da aiki kan hanyoyin tabbatar da tsaron kayayyakin noma da saukaka jigilar su daga wuraren da ake samarwa zuwa kasuwanni a dukkan jihohin kasar.