Hukumar gudanarwar Gidan Rediyon jihar Kano ta ƙara kaimi wajen gudanar da shirye-shiryen wayar da kan al’umma muhimmancin karbar rijistar zabe domin tabbatar da cewa dukkan ‘yan ƙasa da suka cancanta sun karɓi katin zaɓensu na dindindin.
Shugaban gidan rediyon, Kwamared Abubakar Adamu Rano, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tattaunawa da ma’aikatan gidan, inda ya ce an fito da sababbin dabaru da za a yi amfani da su wajen yaɗa saƙon wannan muhimmin aiki.
Kwamared Rano ya bayyana farin cikinsa bisa yabon da gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya yi wa gidan Radiyon kan yadda yake gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a kan batun rijistar masu zaɓe. Ya ce gwamnan ya nuna matuƙar gamsuwa da ƙoƙarin da gidan rediyon ke yi a wannan fanni.
Gidan Radio Pyramid zai yi aikin hadin gwiwa da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta jihar Kano
Shugaban ya ƙara da cewa gidan rediyon ya mai da yawancin shirye-shiryensa kan wannan batu saboda muhimmancinsa ga ci gaba da dorewar dimokuraɗiyya. Ya bukaci ma’aikatan gidan da su fito da ƙarin dabaru da za su ƙara ƙarfafa gwiwar jama’a wajen karɓar katin zaɓensu.

A cewar sa, “Gidan Rediyon Kano ya dade yana kan gaba wajen yaɗa shirye-shiryen da ke kawo cigaban al’umma, kuma za mu ci gaba da riƙe wannan matsayi ta hanyar ƙoƙari da shirye-shirye na musamman.”
Kwamared Rano ya godewa gwamnan bisa yabon da ya yi musu tare da tabbatar da cewa za su ƙara himma wajen cika wannan muhimmin aiki. Haka kuma ya jinjinawa kwamitin jihar ƙarƙashin jagorancin kwamishinan yaɗa labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, bisa jajircewarsa kan aikin da Gwamna ya dora masa, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tsayawa tsayin daka akan duk abun da ya shafi cigaban al’umma.