Alkalin Kotun Majistare da ke gudanar da shari’ar masu karya dokokin hanya a birnin Kano ya ayyana wani direba mai suna Bashir Fagge a matsayin wanda ake nema, bayan ya tsere daga gaban kotun tafi-da-gidanka.
DAILY TRUST to a rawaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 2 ga Satumba, 2025, lokacin da Bashir Fagge, wanda yake tuƙa mota mai lambar KMC 302 BD, ya karya doka ta hanyar ƙin biyayya ga fitilun bada hannu. Wannan ya saba da Sashe na 16(4), (7), da (8), sakin layi na 12 na Dokar KAROTA ta 2012.
Daga bisani akq gayyace shi da ya bayyana a gaban Kotun Tafi-da-gidanka ta KAROTA da ke kan titin Ibrahim Taiwo, kusa da otal din Gab domin fuskantar shari’a, amma ya ki bayyana.
Saboda haka, alkalin da ke jagorantar shari’ar ya bayar da umarni cewa dole ne Bashir Fagge ya bayyana a gaban kotu ba tare da ɓata lokaci ba, a ranar ko kafin Talata, 16 ga Satumba, 2025.
Rijistar Zabe: Gidan Rediyon Kano Ya Ƙara Zage Dantse Wajen Wayar da Kai Kan Al’umma
Kotun ta gargade shi cewa rashin bayyana zai sa a bayar da samun takardar kama kai tsaye (bench warrant) domin cafke shi nan take.
A wata sanarwa, Jami’in Hulɗa da Jama’a na KAROTA, Abubakar Ibrahim Sharada, ya tunatar da cewa hukumar ta kaddamar da kotunan tafi-da-gidanka a manyan tituna da kananan hanyoyi a Kano domin shari’ar masu karya dokokin titi.

Ya ce wannan mataki an ɗauke shi ne sakamakon yawan take dokokin fitilu da alamu na hanya da masu mota, masu keke Napep, da sauran masu amfani da hanya ke yi, wanda sau da yawa kan haifar da rauni, asarar rayuka, da lalacewar dukiya.