Hukumar Hisbah ta Karamar Hukumar Birni a Jihar Kano ta tura jami’anta sama da 1,000 domin tabbatar da tsaro a yayin bikin Takutaha, tare da fatattakar batagari da ke fakewa da bikin wajen aikata ayyukan da suka saba wa addini da al’ada.

Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar Birni, Ustaz Hamidan Tanko Alasaka, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya aikowa Kadaura24 a Kano.
Ya ce jami’an da aka tura sun haɗa da na musamman da za su kula da tsaro, tsafta, da kuma bin ka’idojin bikin, tare da tabbatar da cewa ba a kawo cikas ba a yayin gudanar da shagulgulan.
Ustaz Alasaka ya ƙara da cewa, a baya ana samun wasu matasa da ke amfani da wannan rana wajen aikata abubuwan da suka sabawa koyarwar addinin Musulunci, lamarin da ya haifar da matsaloli.
“Saboda haka ne muka ɗauki ƙwararan matakai domin tabbatar da cewa an gudanar da bikin cikin tsaro, natsuwa da kuma mutunta dokokin addini,” in ji kwamandan.