Gwamnatin Jihar Kano ta kaddamar da Majalisar Shurah wacce za ta riƙa bayar da shawarwari domin inganta tafiyar da mulki tare da samar da ci gaba mai ɗorewa ga al’umma.
An gudanar da bikin kaddamarwar ne a gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa kafa wannan majalisa na daga cikin dabarun gwamnatinsa na tabbatar da shugabanci na gaskiya, adalci da kuma shigar da jama’a cikin tafiyar da mulki.

A cewar gwamnan, Majalisar za ta mayar da hankali wajen bayar da shawarwari a muhimman fannoni kamar tattalin arziki, ilimi, lafiya, tsaro da walwalar al’umma. Ya ce gwamnatin Kano na da burin ƙarfafa hanyoyin da za su bai wa jama’a damar tofa albarkacin bakinsu domin ci gaban kowa da kowa.
Tun da farko, Sakataren Majalisar Shurah, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya sanar da nadin Wazirin Kano, Sheikh Sa’ad Shehu Gidado, a matsayin Shugaban majalisar, tare da Farfesa Sani Zaharaddeen a matsayin mataimaki, sannan sauran mambobi 67 da suka haɗa da malamai, ’yan kasuwa, kwararru da wakilan al’umma daga kowane yanki na jihar.
Kadaura24 ta rawaito cewa kafa wannan majalisa zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban al’umma da kuma shugabanci na gaskiya da rikon amana a jihar Kano.