Ibtila’in: Tsawa ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da jikkata wata a Kano

Date:

Wani mummunan lamari ya auku a ƙauyen Ƙogi Fulani da ke cikin karamar hukumar Gezawa, Jihar Kano, inda mutane biyu suka rasa rayukansu sakamakon bugun tsawa.

Wadanda suka rasu sakamakon ibtila’in akwai Basiru Muhammad da Salamatu wadanda duk yan gida Daya ne, sai kuma Hafsat Muhammad wadda ta jikkata.

Malam Muhammad shi ne mahaifin Basiru ya tabbatarwa da Kadaura24 faruwar Lamarin , inda ya ce sun kado Sosai da yadda suka ga Gawar Dan nasu.

Iyalan waɗanda abin ya shafa, sun tabbatar da faruwar wannan musiba, tare da bayyana alhini da bakin cikin da suka shiga.

Za mu yi Aiki ba Dare ba Rana domin Tabbatar da Umarnin da Ganduje ya ba mu – Baffa Babba Dan’agundi

“A jiyama lokacin da abun ya faru sai da Basiru ya yi aikin hatsi daga bisani kuma Ina alwala kawai sai na ganshi ya fadi Kasa kan ka ce kobo Allah ya karbi kayansa , Amma abun mamakin sai da kayan jikinsa suka kone Gaba Daya”.

” Basiru dana ne , kuma mun karbi wannan ibtila’in da Allah ya aiko mana , kuma muna Addu’ar Allah ya gafarta musu yasa Aljanna ta zamo makomarsa”.

Haka ita ma mahaifiyar Salamatu ta ce ta kadu matuka bisa yadda tsawa ta yi sanadiyyar rasuwarta .

FB IMG 1753738820016
Talla

A halin da ake ciki, hukumomi sun shawarci al’umma da su yi taka-tsantsan da yanayin ruwan sama mai haduwa da tsawa, domin kare rayuka da lafiyarsu.

Dama dai hukumar Kula da hasashen yanayi ta Nigeria (NIMET) ta yi hasashen za a iya samun irin wannan yanayin na tsawa da mamakon ruwan sama, don haka ta shawarci al’umma da su rika kaucewa wuraren da za’a iya samun irin wannan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...