Ku rika amfani da Sabon tsarin koyarwa da gwamnatin Kano take daukar nauyin koya muku – Sakataren Ilimin Kiru ga Malaman Firamare

Date:

Daga Shehu Hussaini Getso

Sakataren Ilimi na Karamar Hukumar Kiru, Alhaji Ayuba Garba Gajale, ya bukaci malaman makarantu na fannin kimiyya da ke cikin kananan hukumomin Kiru, Bebeji, Tudun Wada, Doguwa, Madobi, Garun Mallam, Karaye da Rogo, da su yi cikakken amfani da sabon tsarin horaswa da Gwamnatin Kano ta samar domin inganta harkokin koyarwa a yankunansu

Alhaji Gajale ya yi wannan kira ne a karshen makon da ya gabata, yayin rufe taron horaswas da aka shirya wa wasu daga cikin malamai a Kafin Miyaki Model Primary School, da ke cikin Karamar Hukumar Kiru.

Ya bayyana cewa aikin koyarwa muhimmin aiki ne da ke da nasaba kai tsaye da ci gaban kowace al’umma, don haka ya bukaci mahalarta taron da su yi amfani da abin da suka koya wajen ilmantar da dalibansu cikin yanayin da ya dace da zamani.

A cewar sa, Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf na baiwa fannin ilimi kulawa ta musamman, musamman wajen samar da kayan koyo da koyarwa, gina sababbin makarantu, da kuma inganta walwalar malamai ta fuskar albashi da karin girma a duk lokacin da ya dace.

A karshe, Sakataren ya yabawa Shugaban Hukumar Ilimin Bai Daya ta Jihar Kano (SUBEB), Alhaji Yusuf Kabir Gaya, bisa cikakken hadin kai da goyon baya da yake bai wa fannin a koda yaushe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...