Daga Safyan Dantala Jobawa
Kungiyar masu amfani da ruwan Haɗejiya da Jama’are (WUA) ta amince da sakatarenta, Alhaji Mustapha Adamu Mudawa, a matsayin sabon shugabanta.
Wannan ya biyo bayan ƙarewar wa’adin shugabancin kungiyar na baya, inda aka gudanar da taron tabbatar da sabon shugabanci a matakai daban-daban domin ƙara kawo ci gaban harkar noma a kogunan Haɗejiya da Jama’are da ke cikin ƙananan hukumomin Kura, Bunkure da Garun Malam.
Kungiyar ta bayyana cewa zaɓen Mudawa ya yi daidai da irin namijin ƙoƙarinsa wajen kare muradun manoma, don haka ta yanke shawarar damƙa masa wannan muƙami domin ƙarfafa cigaban manoman yankin.
Da yake jawabi, sabon shugaban, Alhaji Mustapha Adamu Mudawa, ya roƙi mambobin kungiyar da su haɗa kai wajen kare muradun manoma da inganta harkar noma kamar yadda aka san kungiyar da wannan aiki tun farko.

Haka kuma, kungiyar ta amince da naɗin Malam Sama’ila Sani Shirye a matsayin mataimakin shugaban kungiyar.
Taron ya samu halartar manoma da dama tare da wakilan shugabanci na kogunan Haɗejiya da Jama’are, inda aka gudanar da shi a ɗakin taro na Haɗejiya da Jama’are da ke karamar hukumar Kura.