Yan Sanda Sun Cafke Masu Damfara Uku da ke Sojan Gona a Kano

Date:

 

 

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta cafke wasu mutane uku da ake zargin suna damfarar mutane tare da yin Sojan gona.

Wadanda aka kama sun haɗa da Nasiru Adamu mai shekara 30 daga Jihar Sokoto, Yusuf Sani mai shekara 49, da kuma Aliyu Yusuf mai shekara 25, dukkansu daga Karamar Hukumar Daura a Jihar Katsina. An kama su ne a ranar 2 ga Satumba, 2025, da misalin karfe 1:30 na rana a unguwar Danagundi, Kano.

Rahoton ‘yan sanda ya nuna cewa sun damfari wani mutum mai suna Salisu Ibrahim kudin da ya kai naira miliyan ɗaya da dubu talatin (₦1,030,000.00), bayan sun yi ikirarin su jami’an tsaro ne kuma suna da wata “ƙwarewa ta musamman” da za su taimaka masa da ita. Sun bukace shi ya kai musu kudin wani wuri inda suka shirya ci gaba da ba shi umarni ta hanyar amfani da sirri.

Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kano ta Fitar da Kudin Ajiya da Adadin Kujerun Hajji na 2026

Bayan samun kiran gaggawa daga wanda abin ya rutsa da shi, da taimakon jama’a, jami’an tsaro suka yi gaggawar kama waɗanda ake zargin. Rundunar ta ce za ta cigaba da gudanar da bincike kuma da zarar an kammala, za a gurfanar da su a gaban kotu.

Kwamishinan ‘Yan Sanda na Kano, CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, ya yaba da yadda jami’ansa suka yi gaggawar Kai dauki da kuma gudunmuwar jama’a wajen kama waɗanda ake zargin. Ya tabbatar da cewa rundunar ‘yan sanda za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin jama’a tare da jajircewa wajen yaki da masu aikata laifuka a fadin jihar.

FB IMG 1753738820016
Talla

Kwamishinan ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani abin da suke zargi, ta hanyar tuntubar ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko kuma kiran lambobin gaggawa na rundunar.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na Rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya aikowa Kadaura24 ya ce Rundunar ta kuma jaddada cewa nasarar da ake samu ta ta’allaka da haɗin kan jama’a da ‘yan sanda, musamman a ci gaba da aiwatar da shirin “Operation Kukan Kura.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...