Pyramid Radio za ta hada hannu da Jami’ar Maryam Abacha don inganta aikin Jarida a Kano

Date:

Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa

Gidan Radio tarayya Pyramid FM zai hada hannu da jami’ar Maryam Abacha dake jihar Kano domin inganta aikin Jarida da magance labaran karya a jihar da Kasa baki daya.

Shugaban gidan Radio Dr. Garba Ubale Danbatta ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar aiki da ya kai jami’ar.

Ya ce aikin Jarida a wannan zamanin na fuskantar kalubale mai yawa saboda zuwa kafafen sada zumunta , saboda yadda kowa ya ke zaman Dan Jarida ba tare da ya Sami Ilimin aikin ba.

” Ina fatan za ku samar da wata dama ga yan jarida da suke aikin domin a rika ba su horo na musamman ko da na watanni Uku zuwa 4 ne sannan ku ba su shederar halartar hoton, Ina ga Wannan zai taimaka matuka wajen kara Samar da kwararrun yan Jarida da kuma magance yada labaran Karya”. Inji Dr. Danbatta

Dr. Garba Ubale Danbatta ya ce gidan Radio Pyramid a shirye yake domin hada hannu da jami’ar ta Kowacce fuska domin magance matsalolin Dan aikin Jarida ke fuskanta a Wannan zamani .

Ya kuma yabawa shugaba kuma mamallakin jami’ar ta Maryam Abacha Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bisa yadda yake amfani da dukiyarsa a fannin Ilimi da kuma tallafawa al’umma ta fuskoki daban-daban a jihar Kano da Nigeria da Africa baki daya.

Al’umma Sun Zargi Shugabannin Babban Asibitin Rano Da Kwashe Kayan Aikin Asibitin

” Tabbas Farfesa Gwarzo ya chanchanchi a yaba masa kuma ya kamata attajiran da muke da su a jihar Kano yi koyi da shi wajen samar da makarantu don samar da al’umma mai cike da Ilimi da kuma taimakawa al’umma a fannonin rayuwa “. A cewar Dr. Danbatta .

Ya kuma yi alkawarin gidan Radio tarayya Pyramid Fm a shirye yake domin baiwa jami’ar Maryam Abacha duk wata gudunmawa da ta ke bukata ta fuskatar yada labarai da sauran aiyukan jami’ar .

Da yake nasa jawabin Shugaba kuma mamallakin jami’ar Maryam Abacha Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo bayan ya yabawa sabon shugaban gidan Radio Pyramid ya kuma da tabbacin jami’ar a shirye take ta hada Kai da gidan Radio Pyramid domin taimakawa al’ummar jihar Kano .

Farfesa Adamu Gwarzo wanda mukaddashinsa Farfesa Ibrahim Maigari ya wakilta ya ce da Shugabanni za su gane da idan suka magance matsalolin da ake fuskanta a bangaren yada labarai, da su magance kaso Mai yawa na matsalolin kasar nan.

FB IMG 1753738820016
Talla

” Ina baka tabbacin za mu aiki tare kuma kofarmu ko da yaushe a bude take domin karbar shawarwari daga kare ku domin mu inganta aiyukanmu, musamman bangarenmu na tsangayar koyar da aikin Jarida”.

Farfesa Gwarzo ya ba da Jami’ar Maryam Abacha za ta yi aiki kafada da kafada da gidan Radio Pyramid fm don inganta aikin yada labarai a jihar Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Karamin Minista Yusuf Ata ya mayarwa da Abdullahi Abbas Martani

Karamin Ministan Ma’aikatar Gidaje da Bunƙasa Birane na tarayyar...

APCn Kano ta Kai karar Minista Yusuf Ata wajen Shugaban Kasa Tinubu

Jam’iyyar APC a Kano ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyya Abdullahi...

‎Gwamnati ta ba da umarnin rufe makarantun kwana 47 a faɗin Najeriya ‎

‎Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun kwana...