Kwamitin da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kafa domin bincikar korar jami’an Hisba da gwamnatin Kano ta yi ya fara zaman sa na farko.
Babban Darakta Janar na Hukumar Samar da Ayyuka ta Kasa, Dr. Baffa Babba Dan’Agundi, shi ne shugaban kwamitin, wanda ya ce sun fara aikin tantance jami’an Hisba da aka sallama daga aiki domin neman musu makoma.
Kwamitin, wanda ya kunshi mutum bakwai, ya amince da kafa wakilai 44 daga kowace karamar hukuma ta jihar Kano domin gudanar da bincike a matakin kasa.
Ribado ya magantu Kan zargin da El-Rufai ya yiwa Gwamnatin tarayya game da yan bindiga
Rahotanni sun ce za a yi amfani da kananan kwamitocin ne wajen tabbatar da gaskiyar korar jami’an Hisba da adadinsu ya kai kusan 1,000 da gwamnatin Kano ta sallama.
Haka kuma, babban kwamitin ya amince da kafa wani kwamiti na mutum uku da zai tabbatar da tsayar da mutum daya daga kowace karamar hukuma domin wakilci a gaba.

A cewar shugabannin kwamitin, za a sake gudanar da wani zama a karshen mako domin karbar rahoton da kananan kwamitoci za su gabatar kafin daukar matakin gaba.