Wata Kotun Majistare a Kano ta bayar da umarni ga mataimakin sufeton yan sanda mai kula da shiyya ta daya da ya gudanar da cikakken bincike kan zargin wasu laifuka da ake yi wa Jafar Jafar, mamallakin jaridar Daily Nigerian dake Kano.
Wannan na zuwa ne bayan karar da Darakta Janar na Mai Kula da Tsare-tsare da tsafiye-tsafiyen Gwamna kano, Hon. Abdullahi Ibrahim Rogo, ya shigar a gaban Kotun Majistare ta 15 da ke Nomansland, ƙarƙashin jagorancin Alkalin kotu, Malam Abdul’aziz M. Habib.
A cikin ƙarar, Rogo ya tuhumi Jafar Jafar tare da wani Audu Umar da laifin batanci da kuma ɓata masa suna ta hanyar Kiran shi da barawo a wani Labari da ya wallafa.

Ƙarar ta dogara ne bisa dokokin shari’a na Kano na shekarar 2019, sassan 106 da 107, da kuma Kundin Laifuka na Kano, sassan 114, 164 da 393, inda ake neman gurfanar da su bisa wallafe-wallafen da aka yi a ranar 22 da 25 ga Agusta, 2025.
A ranar 25 ga watan Agusta, jaridar Daily Nigerian ta wallafa wani rahoto mai taken: “Gov. Yusuf Defends Thieving Aide, Says Protocol Directorate Under Ganduje Spent N20 Billion in 3 Months”, wanda mai ƙara ya ce an tsara shi ne da gangan don tozarta shi da bata masa sunansa.
Haka kuma, a ranar 22 ga watan Agusta, jaridar ta sake wallafa wani labari da ya ce: “Court Documents Reveal How ICPC, EFCC Traced N6.5 Billion to Gov. Yusuf’s DG Protocol”, abin da mai ƙara ya bayyana a matsayin ƙarya da ɓatanci da aka yi masa.
Mai ƙarar ya shigar da ƙarar tuhuma guda biyu a kan Jafar Jafar da abokin tuhumarsa, wacce ta shafi batanci a ƙarƙashin sashe na 393 na Kundin Laifuka da kuma tada hankalin jama’a a ƙarƙashin sashe na 114.
Alkalin kotun ya umarci Mataimakin sufeton ‘yan Sanda mai kula da Shiyya ta Ɗaya, dake Kano, da ya gudanar da cikakken bincike kan labaran da aka wallafa. Wannan umarni ya fito ne daga kotu a ranar 28 ga Agusta, 2025.
A gefe guda, an kuma shigar da wata ƙara na daban a gaban Babbar Kotun Kano, inda ake neman diyya daga Jafar Jafar da jaridar Daily Nigerian bisa zargin bata sunan Abdullahi Ibrahim Rogo.
Gwamnatin Kano ta ce zarge-zargen da ake yadawa kan DG Protocol yan adawa ne kawai suke kitsasu domin batawa gwamnatin suna.
Haka kuma, kotu ta umurci ‘yan sanda da su binciki dalilin da yasa Jafar Jafar ya kauce wa ƙa’idar aikin jarida ta hanyar yanke hukunci kan binciken da bai kammala ba tare da kiran wani jami’i “barawo” saboda kawai ICPC tana bincikarsa.