EFCC ta tsare dan’uwan shugaban NAHCON kan zarginsa da hannu a badakalar Naira Biliyan 50

Date:

Hukumar Yaki da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Zagonsa (EFCC) ta tsare ɗan’uwan shugaban Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON), Sirajo Salisu Usman, bisa zarginsa da hannu cikin badakalar Naira biliyan 50 a kudaden aikin Hajji.

Sirajo, wanda ake yi wa lakabi da “ka fi chairman” saboda tasirinsa a hukumar, shi ne ɗan’uwan Farfesa Abdullahi Saleh Usman, wanda aka fi sani da “Pakistan”, shugaban NAHCON. Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun cafke shi a Abuja ranar Laraba, inda ya kwana a tsare.

FB IMG 1753738820016
Talla

Sirajo, wanda ke matsayin Mataimakin Darakta a ofishin shugaban hukumar, ya sha amsa tambayoyi tun farkon wannan watan tare da wasu manyan jami’an NAHCON.

Binciken EFCC ya danganta shi da asarar Naira biliyan 25 wajen biyan kudin tantunan Masha’ir, Naira biliyan 8 wajen gidajen ajiyar mahajjata a Makka, da kuma Naira biliyan 1.6 da aka kashe wajen daukar matan jami’an NAHCON a shekarar 2025 kadai.

Da dumi-dumi: Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Jaridar Daily Nigerian Jafar Jafar a gaban Kotu

Rahotanni sun kuma tabbatar da cewa hukumar ta sayi masaukin gaggawa 6,500 a Makka da ba a yi amfani da su ba, abin da ya janyo asarar kusan Naira biliyan 8.

Tun daga 7 ga watan Agusta, EFCC ta sha tambayar wasu manyan jami’an hukumar, ciki har da lauyin NAHCON, Barrister Nura Danladi, da kuma wasu daraktoci. A ranar 19 ga watan nan, hukumar ta kuma tsare wasu kwamishinoni biyu, ciki har da na kudi da tsare-tsare.

Wani rahoto na cikin gida ya bayyana cewa harkokin kudi a NAHCON na tafiya cikin “gagarumin gazawa”, tare da zargin karin kudi da almubazzaranci da kudin ya haura Naira biliyan 4.

Wani jami’in hukumar ya shaida wa Daily trust cewa, “Duk wata takardar hukuma Sirajo ne ke yi wa shugaban bayaninta kuma shi ke sanya hannu. Wannan ne ya sa ma’aikata ke kira ga EFCC ta gudanar da cikakken binciken kan duk wani umarni da shugaban ya bayar.”

Kiraye-kirayen gyaran NAHCON
Masu ruwa da tsaki sun nemi a yi wa hukumar NAHCON garambawul, inda suka bukaci a sallami shugaban da duk wanda aka samu da hannu a barnar, tare da neman dawo da dukiyar al’umma da ta salwanta.

Har wa yau, ma’aikatan hukumar sun yi barazanar shiga yajin aiki idan shugaban bai sake jami’an da aka ajiye a ofishinsa ba, tare da yin adawa da shirin dawo da wasu tsofaffin ma’aikatan da aka kora daga aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tinubu ya taya tsohon Gwamnan Kano, Shekarau murnar cika shekaru 70

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon Gwamnan...

Abdulmumin Kofa ya koma APC tare da bayyana goyon bayansa ga Tinubu

Abdulmumin Jibri Kofa, ɗan majalisar wakilai mai wakiltar Kiru...

Labari mai dadi: Nahcon ta rage kudin kujerar hajjin 2026

Shugaban hukumar NAHCON Kula da aikin hajji ta Nigeria ...

Shugabannin Hukumomi a Kano Sun Yaba Da Ayyukan Abba, Sun Nemi Ya Nemi Wa’adi Na Biyu

Kungiyar shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnatin jihar Kano ta...